Zaben Anambara: Ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015?2
Ya zuwa yanzu dai kowa ya ji ko yana sane da yadda aka gudanar da zaben Jihar Anambara da irin tirka-tirkar da ta bayyana. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da wannan zabe, ko INEC za ta iya gudanar da sahihi kuma amsasshen zabe a 2015? Wakilanmu sun tuntubi mutane kuma […]
Ya zuwa yanzu dai kowa ya ji ko yana sane da yadda aka gudanar da zaben Jihar Anambara da irin tirka-tirkar da ta bayyana. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da wannan zabe, ko INEC za ta iya gudanar da sahihi kuma amsasshen zabe a 2015? Wakilanmu sun tuntubi mutane kuma ga abin da suke cewa:
Zabe mai inganci zai yi wuyar samu – Musa Yobe
Kabir Yayo Ali, a Ibadan
Musa Yobe: “Zai yi wuyar gaske INEC ta iya gudanar da zabe mai inganci a 2013, domin ba ta sauraron koke-koken jama’a a wuraren da aka samu magudin zabe sai abin da ta ga dama take yi. Idan muka lura da zaben da aka yi a Jihar Anambra, wani mai sharhi a kan al’amura mai suna Dino Melaya ya yi binciken kwakwaf da ya gano aringizon kuri’u fiye da dubu 80, sama da jimillar yawan kuri’un da INEC ta ce an jefa kuma bai iya gano jam’iyyar da ta mallake su ba. Ka ga ke nan a fili ya nuna cewa INEC ba za ta iya gudanar da ingantaccen zabe a 2015 ba.”