Zaben Anambara: Ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015?4
Ya zuwa yanzu dai kowa ya ji ko yana sane da yadda aka gudanar da zaben Jihar Anambara da irin tirka-tirkar da ta bayyana. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da wannan zabe, ko INEC za ta iya gudanar da sahihi kuma amsasshen zabe a 2015? Wakilanmu sun tuntubi mutane kuma […]
Ya zuwa yanzu dai kowa ya ji ko yana sane da yadda aka gudanar da zaben Jihar Anambara da irin tirka-tirkar da ta bayyana. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da wannan zabe, ko INEC za ta iya gudanar da sahihi kuma amsasshen zabe a 2015? Wakilanmu sun tuntubi mutane kuma ga abin da suke cewa:
INEC Ba za ta iya ba – Mustapha Tukur
Isa Muhammad Inuwa, a Kano
Mustapha Tukur: “Ra’ayina a nan shi ne cewa, zaben Anambra ya nuna cewa INEC ba za ta yi wani zabe mai inganci ba a 2015. Dalilina a nan kuwa shi ne, tun farko ma a ina aka yi tanadin sake yin wani ciko na zabe? Idan an san tun farko ba a shirya yadda ya kamata ba, ai bai kamata a fara yin zaben ba, bare ma a wannan zaben sai da aka kai tarin jami’an tsaro har da shugabanninsu. To idan haka za ta faru a jiha daya kawai, ina kuma idan dukkanin jihohi 36 ne na kasar nan? Kirana ga hukumar zabe shi ne, ta sake tsarkake zuciyarta da niyyarta wajen yin zabe na gaskiya. Amma yanzu ba ta shirya yin hakan ba.”