Zaben Anambara: Ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015?5

Ya zuwa yanzu dai kowa ya ji ko yana sane da yadda aka gudanar da zaben Jihar Anambara da irin tirka-tirkar da ta bayyana. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da wannan zabe, ko INEC za ta iya gudanar da sahihi kuma amsasshen zabe a 2015? Wakilanmu sun tuntubi mutane kuma […]

Zaben Anambara: Ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015?5
Zaben Anambara: Ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015?5

Ya zuwa yanzu dai kowa ya ji ko yana sane da yadda aka gudanar da zaben Jihar Anambara da irin tirka-tirkar da ta bayyana. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da wannan zabe, ko INEC za ta iya gudanar da sahihi kuma amsasshen zabe a 2015? Wakilanmu sun tuntubi mutane kuma ga abin da suke cewa:

Zabe nagari zai wuya a 2015 – Ayuba Idris
Isa Muhammad Inuwa, a Kano

Ayuba Idris Panshekara: “A gaskiya dukkan alamu sun nuna cewa INEC ba za ta yi zabe nagari ba a 2015 saboda abin da ya faru a zaben Anambra ya nuna hakan. Mun ga irin wannan ta faru a Jihar Kano a zaben cike gurbi na marigayan ’yan majalisar jiha daga Garko da Gaya, inda aka kyale hukumar zabe ta jiha ta shirya magudi amma daga baya hukumar zabe ta kasa ce ta sanar da sakamakon zaben, bayan an tauye wa ’yan jam’iyyun adawa hakkinsu.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi