Zaben Anambara: Ko INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015?7
Ya zuwa yanzu dai kowa ya ji ko yana sane da yadda aka gudanar da zaben Jihar Anambara da irin tirka-tirkar da ta bayyana. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da wannan zabe, ko INEC za ta iya gudanar da sahihi kuma amsasshen zabe a 2015? Wakilanmu sun tuntubi mutane kuma […]
Ya zuwa yanzu dai kowa ya ji ko yana sane da yadda aka gudanar da zaben Jihar Anambara da irin tirka-tirkar da ta bayyana. Abin tambaya a nan shi ne, idan muka yi la’akari da wannan zabe, ko INEC za ta iya gudanar da sahihi kuma amsasshen zabe a 2015? Wakilanmu sun tuntubi mutane kuma ga abin da suke cewa:
Jama’a sun dawo daga rakiyar INEC – Aminu Baba
Hussaini Isah, a Jos
Aminu Baba: “Batun INEC za ta iya gudanar da sahihin zabe a 2015 ko ba za ta iya ba, kan zaben da aka gudanar a Jihar Anambara, bai taso ba. Domin tuni jama’a sun dawo daga rakiyar hukumar. Don haka a duk lokacin da hukumar zabe ta shirya zabe, jama’a kowa sai ya zauna a gida ya ki fita. Shi ya sa ko a zaben da aka gudanar a Jihar Anambara, kashi biyu bisa uku na jama’ar da suka yi rijista, ba su fito sun yi zabe ba. Don haka hukumar zaben ta kasa, ba za ta iya gudanar da zabe sahihi ba a 2015.”