Zaben Badi: Ko ’Yan Sanda Za Su Yi Wa Jam’iyyun Adawa Adalci?
A Watan Fabrairun badi ne ake sa ran gudanar da zabe a matakai daban-daban na mukaman siyasa. Jami’an tsaro, musamman ma ’yan sanda suna da babbar rawar da za su iya takawa. La’akari da yadda suke gudanar da ayyukansu a yanzu, shin ko ’yan sandan za su iya yi wa jam’iyyun adawa adalci kuwa? Ga […]
A Watan Fabrairun badi ne ake sa ran gudanar da zabe a matakai daban-daban na mukaman siyasa. Jami’an tsaro, musamman ma ’yan sanda suna da babbar rawar da za su iya takawa. La’akari da yadda suke gudanar da ayyukansu a yanzu, shin ko ’yan sandan za su iya yi wa jam’iyyun adawa adalci kuwa? Ga abin da jama’a ke fadi kan al’amarin:
Babu alamar za su yi adalci – Kabiru Hussaini
Hussaini Isah a Jos
Alhaji Kabiru Hussaini: ‘’A gaskiya babu alamar jami’an tsaro za su yi wa jam’iyyun adawa adalci a zaben badi, domin tun yanzu ga rashin adalcin da shugaban ’yan sandan Najeriya, Alhaji Abba Sulieman ya fara nunawa kan shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal; a inda ya ba da umarni a hana shi shiga majalisa kuma ya ce shi bai san shi ne shugaban majalisar ba. Wannan ya nuna cewa jami’an tsaro za su yi aiki ne da umarnin da jam’iyya mai mulki za ta ba su. Don haka babu maganar za su yi adalci a zabe mai zuwa.
Babu alamar za su yi adalci – Mahe Kwaftara
Hussaini Isah, a Jos
Alhaji Mahe Kwaftara: ‘’Maganar jami’an tsaro su yi wa jam’iyyun adawa adalci a zaben badi, ba ta taso ba, domin a yanzu jami’an tsaron kasar nan suna aiki ne tare da gwamnati. Yanzu a kasar nan ana tura jami’an tsaro zuwa ko’ina ne don su kare gwamnati, amma ba don su tsare lafiyar talakawan kasa ba. Jam’iyyun adawa babu masu son su sai talakawa, don haka ba za su taba samun adalci ba daga wajen jami’an tsaron kasar nan a zaben badi. Sai dai jam’iyyun adawa su tashi su kare kuri’un da talakawa za su jefa masu amma ba jami’an tsaro ba.”
Alama ta nuna ba za su yi adalci ba – Darda’u Abdu
Isa Muhammad Inuwa, a Kano
Darda’u Abdu Ya-salam: “To mu a bisa tsarin da muke fuskanta a halin yanzu, babu maganar adalci da za a samu daga jami’an tsaron kasar nan, wanda za su nuna wa jam’iyyun adawa. Dalilina a nan shi ne, irin son kai karara da suke fitowa fili suna nunawa wajen goyon bayan gwamnati. Daga nan ma za mu gane cewa idan zaben ma ya zo haka za su goya baya ga jam’iyya mai mulkin kasar nan. Mu kuma muna ganin hakan bai dace ba, domin kuwa su ba ’yan siyasa ba ne amma sun mayar da kansu ’yan siyasa kuma karnukan farautar masu mulki. Ko a kwanakin nan rigima tsakanin jami’an tsaro da majalisar kasa ta nuna haka kowa ya gani kuma mun san komai.”
Jam’iyyun adawa ba za su samu adalci ba – Yahaya Abdullahi
Isa Muhammad Inuwa, a Kano
Yahaya Abdullahi: “Mu talakawa mun riga mun gane cewa babu adalci a tsakaninmu da masu mulkinmu, haka nan babu wani adalci da jami’an tsaro za su yi ga jam’iyyun adawar kasar nan a zabe mai zuwa. Daga abin da ya faru na hana shugaban Majalisar Wakilai da sauran ’yan majalisa, muka gane cewa jami’an tsaron nan ga inda suka dosa, wato rashin adalci da goyon bayan gwamnati mai mulki da jam’iyya mai mulki. Ko sun yi daidai, ko ba su yi daidai ba, kowa ya ga inda suka sa gaba kuma abin da suke so ke nan, su yi ta mulkinmu babu adalci. Amma duk da haka ba za mu fasa fitowa mu jefa kuri’a ba, domin mun san Allah Yana tare da mu, kuma Shi zai goyi bayanmu.”
Jami’an tsaro ba za su iya adalci ba -Shu’aibu Mahmud
Kabir Yayo Ali, a Ibadan
Shu’aibu Mahmud Kyaudai: “Yan sanda a Najeriya ba su da ’yancin gudanar da aikinsu sai abun da aka umurce su da yi. Saboda haka nake ganin ba za su iya yin adalci ga masu hamayya da iyayen gijinsu a zaben shekara ta 2015 ba. Idan ka lura sosai da irin danyen aikin da ’yan sanda suka tafka ga mutum na 4 a mulkin kasar nan, wato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, da suka jefa masa hayaki mai sa hawaye a lokacin da yake so ya shiga majalisar da yake shugabanta, sai ka ga cewa babu wani adalci da jami’an tsaro za su yi a zabe mai zuwa.”
Babu tabbacin samun adalci a zaben – Dauda Muhammad
Kabir Yayo Ali, a Ibadan
Malam Dauda Muhammad: “Tsakanina da Allah ba ni da tabbacin jami’an tsaro za su yi wa ’yan adawa adalci a zabe mai gabatowa saboda ina kallon jam’ian tsaro ne a matsayin ’yan karen farautar gwamnati; sai abun da aka ce su yi suke yi. Abu guda daya ne kawai zai yi maganin irin wannan al’amari a lokacin zaben. Shi ne talakawa su fito kwai da kwarkwata ba tare da nuna kwadayi ba, su yi amfani da kuri’unsu wajen nema wa kansu ’yanci. Na taba jin wani mutumi yana cewa kuri’arsa ta sayarwa ce. Ina so jama’ar kasar nan su dawo daga rakiyar zaben mutane da suke raba musu kudade da kayan abinci, su zabi mutanen kwarai domin su girbi alheri a rayuwarsu.”