Zaben Bana: Ko Na’urar Tantance Kati Ta Yi Tasiri Kuwa?

A ranakun Asabar da Lahadi da suka gabata ne aka gudanar da zabubbukan Shugaban kasa da na Majalisun Tarayya a Najeriya, inda aka yi amfani da na’urar tantance kati. Abin tambaya a nan shi ne, daga yadda na’urar nan ta gudanar da aikinta, shin ko ta yi tasiri a zaben? Ga abin da jama’a ke […]

Zaben Bana: Ko Na’urar Tantance Kati Ta Yi Tasiri Kuwa?
Zaben Bana: Ko Na’urar Tantance Kati Ta Yi Tasiri Kuwa?

A ranakun Asabar da Lahadi da suka gabata ne aka gudanar da zabubbukan Shugaban kasa da na Majalisun Tarayya a Najeriya, inda aka yi amfani da na’urar tantance kati. Abin tambaya a nan shi ne, daga yadda na’urar nan ta gudanar da aikinta, shin ko ta yi tasiri a zaben? Ga abin da jama’a ke cewa:

Na’urar ta magance magudi – Usman Ibrahim

A.A. Masagala, a Benin

Alhaji Usman Ibrahim: “Ni a ganina da abin da kuma na fahimta, na farko idan har muna son mu sani aiki da wannan na’uran ya samar da nasara ko a’a, to lallai dole mu waiwaya mu duba irin zabukan da aka rika shirya mana na can baya, mai cike da murdiya da magudi; ba don komai ba illa rashin bin tsari irin na zamani. Saboda haka a yanzu muna iya mu ce an kama hanyar toshe duk wata kafar magudi da aringizon kuri’a a zabukan kasar nan daga sama har kasa.
“Akwai alama da farko, in ba don da an kawo wannan tsari na aiki da nau’rar ba to lallai irin magudin da za a tabka a zaben kasar nan na wannan karon sai ya wuce tunanin kowa; domin zai iya ya nunka na shekarun baya da aka sani.

Na’urar ta yi amfani – Adamu Jigawa

A.A. Masagala, a Benin

Malam Adamu Jigawa: “Ni a Ra’ayina, wannan nau’rar ta yi amfani amma kawai abin da ya rage mata armashi shi ne, wasu daga ciki sun kasa biya wa mutane bukata. Wannan kuma ko kasashen da suka ci gaba ana samun irin matsalar don haka wannan tsarin ya yi amfani kuma an samu nasara. Idan muka yi la’akari da lokacin da aka bullar da wannan shirin da kuma kwarewarmu a kan aiki da ita a lokaci mai kamar wannan, sai mu ce babu laifi domin dole a samu wasu kura-kurai da ba a rasawa saboda ajizanci na dan Adam amma kuma an samu nasara.
“A yadda nake gani, nasara ta farko, an kawar da hanyar magudi da wasu suka saba suna yi a zaben kasar nan kuma da wannan tsarin an rage zarge-zargen juna da satar kuri’u na mazabu kuma za a tantance kuma a gane ainihin mutane nawa ne na gaskiya.

Na’urar ta yi matukar tasiri – Abdulrahman Saleh

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Abdulrahman Saleh: “A ganina, na’urar nan ta tantance masu kada kuri’a da hukumar zabe ta fara amfani da ita a zaben Shugaban kasa da ya gabata, ta yi matukar tasiri dari-bisa-dari. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, duk wurin da aka yi amfani da wannan na’ura ta tantance masu kada kuri’a a yayin zabe, al’ummomin da suka yi zaben sun samu natsuwa matuka, domin suna da yakinin cewar lalle ba za a yi musu magudi ba. Don haka amfani da wannan na’ura ta ta haifar da da mai ido matuka.”

Kwalliya ta biya kudin sabulu – Ahmadu Gajimi

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Malam Ahmadu Gajimi: “A ganina, amfani da wannan na’ura ta tantance masu kada kuri’a da hukumar INEC ta fara amfani da ita, hakika kwalliya ta biya kudin sabulu. Dalili kuwa shi ne, amfani da na’urar ya haifar da keke da keke wajen samar da alkaluma sahihai da babu aringizo ko kadan kuma al’umma sun samu natsuwa dangane da duk wani sakamakon da ya zo musu; kasancewar babu rufa-rufa tattare da zaben. Don haka amfani da wannan na’ura ta tantance masu kada kuri’a abin alfahari ne ga hukumar zaben kasar kanta da ma gwamnatin kasa.

Katin ya yi amfani – Abdulkadir Usman

Rabilu Abubakar, a Gombe

Abdulkadir Usman: “Lallai katin tantance kuri’a ya yi amfani a wannan zaben, domin ya hana magudin zabe ba kamar na shekarar 2011 ba. Duk wanda ya jefa kuri’a a wanann zaben sai da aka tantance shi kuma wannan tantancewar ta kawo sauki na hana magudin zabe da kamar kashi hamsin cikin dari. Da ba a tantance mu kafin mu kada kuri’a ba da ’yan Kudanci Najeriya sai sun kawo kuri’u harda na rashin hankali.”

Na’urar ta yi amfani sai dai…
– Auwal Laleko

Rabilu Abubakar, a Gombe

Alhaji Auwal Laleko: “Lallai wannan nau’ra ta tantance katin zabe kafin a yi zabe ta yi rana sai dai yana da kyau a gyara matsalar da aka rika fuskanta saboda zabe na gaba. Amfani da wannan na’ura sabuwar hanya ce a wajenmu kuma an samu matsaloli na netwok a wasu wurare, wanda hakan ya jawo tsaikon gama zabe a kan lokaci. Zan yi kira ga hukumar zabe da cewa don Allah a gyara matsalolin da aka fuskanta yanzu saboda zabe na gaba ya zo mana cikin sauki kuma ka ga idan lokaci ya yi ba za mu dauke ta a matsayin sabon abu ba saboda mun saba.”