Zaben bana: Yarfen da gwamnati da ’yan adawa ke yi wa juna na kara muni

Dimbin ’yan siyasa masu takara neman mulki daga matakin kasa zuwa jihohi sun yi watsi da kamfe kan abubuwan da suka shafi ci gaban kasa da al’umma kamar yaki da talauci ko farfado da ilimi da kiwon lafiya da sauran abubuwan more rayuwa sun mayar da hankali wajen yi wa juna yarfe. Akalla akwai ’yan […]

Zaben bana: Yarfen da gwamnati da ’yan adawa ke yi wa juna na kara muni

Dimbin ’yan siyasa masu takara neman mulki daga matakin kasa zuwa jihohi sun yi watsi da kamfe kan abubuwan da suka shafi ci gaban kasa da al’umma kamar yaki da talauci ko farfado da ilimi da kiwon lafiya da sauran abubuwan more rayuwa sun mayar da hankali wajen yi wa juna yarfe.

Akalla akwai ’yan takara sama da dubu ashirin dake fafatawa a zaben bana da za a fara gudanarwa a tsakiyar watan gobe.

Cikinsu akwai ’yan takarar Shugaban Kasa 73 wadanda suka fito daga yankuna shida na kasar nan.

A yanzu dai hankalin al’ummar Najeriya ya karkata ne kan yadda zaben Shugaban Kasa zai kaya, kuma ana kyautata zaton cewa daga Arewa zai fito fito.

Kuma duk da cewa a Arewar akwai ’yan takarar Shugaban Kasa da dama, masu fashin baki suna ganin cewa fafatawar ta fi zafi ne a tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP.

Duk da cewa hidindimun kamfe din APC da PDP ba su kankama da wuri ba, kamar yadda aka yi a shekarar 2015, lokacin da Janar Buhar ya fafata Shugaban Kasa a lokacin, Dokta Goodluck Jonathan na PDP, lamarin ya canja a ’yan kwanakin nan inda ’yan takarar biyu da mukarrabansu suka tashi tsaye suna yawo gari-gari suna kamfe domin neman kuri’a daga ’yan Najeriya.

 

Yadda ake yarfe a tsakanin abokan takara

Shugaba Buhari wanda ya kaddamar da kamfe dinsa a garin Uyo da ke Jihar Akwa Ibom, tuni ya zaga wasu yankuna da jihohi kamar Kaduna da Kogi da Bauchi da  Edo da Delta da Neja da Filato da Borno da Yobe da Sakkwato da kuma Kebbi.

Ana kuma sa ran zai ci gaba da zagayawa sauran jihohi kamar Kano da Anambra da Lagas da sauransu. Jadawalin kamfe din APC ya nuna cewa Shugaba Buhari zai je kamfe a jihohi 36 na kasar nan kafin a rufe kamfe.

Masu fashin bakin siyasa suna ganin cewa in dai yawan jama’ar da ke fitowa filayen kamfe ne mizanin da zai nuna tagomashin dan siyasa, to Shugaba Buhari ya samu, domin kusan duk garin da ya je al’amuran yau da kullum suna tsayawa cik, kuma filayen tarurrukan suna cika su batse da jama’a.

A lokacin da Buhari ya je Jos fadar Jihar Filato, ko magana bai yi ba saboda yawan jama’ar da suka yi dango a filin wasa na Rwang Pam.

Haka duk da ana tsoron cewa ’yan ta’adda suna iya aikata aika-aika, dimbin mutane sun tarbe shi a biranen Maiduguri da Damaturu da ke jihohin Borno da Yobe.

To sai dai jam’iyyar adawa ta PDP ta ce wannan ba wani abu a zo a gani ba ne, inda ta bayyana cewa abin da take tsoro shi ne Buhari ya tsufa tukuf, kuma bai san abubuwan da suke gudana ba.

Jam’iyyar PDP, ta ce wadansu tsirarun ’yan siyasa ne suke murda akalar mulkinsa. Kakakin Jam’iyyar PDP, Mista Kola Ologbondiyan, ya yi misali da subutar baki da Shugaba Buhari yayi a birnin Warri da ke Jihar Delta, lokacin da zai bayar da tuta ga Cif Great Ogboru, dan takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC.  Shugaba Buhari cewa yayi “Ina mai farin cikin bayar da wannan tuta ga dan takarar Shugaban Kasa,” maimakon ya ce “dan takarar Gwamna.”

Bayan an gyara masa sai ya kara da cewa “dan takarar Sanata,” aka sake gyara masa sannan ya ya ce “dan takarar Gwamna.” PDP ta ce wannan ba karamar gazawa ba ce.

“Hakika wannan subutar baki ya nuna cewa Buhari ya gaji kuma ba zai iya mulki ba,” inji Kakakin PDP.

“Ya kamata a bar shi ya tafi Daura ya huta domin ko ya ci ma ba zai iya tabuka komai ba,” inji shi.

Kola ya ce tabbas Buhari ya razana, kuma subutar bakin da ya yi ya nuna kamar ya farka daga mafarki ne a ranar da zai mika mulki ga Jam’iyyar PDP.

Kuma har wa yau PDP ta zargi APC da rashin tabuka abin a zo a gani a shekara uku da rabi da suka gabata. “Har yanzu abin da ke fitowa daga bakin Buhari shi ne zai yi maganin rashin zaman lafiya da ta’ddanci, zai yi yaki da cin hanci da rashawa, kuma zai gyara tattalin arziki, amma har yanzu ba mu ga komai a kasa ba,” inji Shugaban PDP Yarima Uche Secondus.

“Wadannan abubuwa da su APC ta yi kamfe a shekarar 2015 amma ba su tabuka komai ba, don haka ’yan Najeriya sun san yaudararsu ake yi kawai,” inji shi.

PDP ta yarfe inda ta zargi gwamnati da Hukumar INEC da kokarin murda zaben bana, ta ce tana da shakku kan gaskiyar INEC kan zaben mai zuwa.

Shi ma dan takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar wanda ya kaddamar da kamfe dinsa a Sakkwato, tuni ya je jihohin Neja da Osun da Ekiti da Ondo da Imo da Jigawa da Kwara da Gombe da kuma Kaduna.

Shi ma yawan jama’ar da suka halarci gangaminsa ba a cewa komai, kuma ya yi alkawura da dama ga jama’a; kamar sake fasalin kasar nan da tabbatar da cewa zai sayar da kamfanin mai na kasa idan ya samu mulki.

To sai dai mabiya Jam’iyyar APC suna zargin Atiku da shirin sayar da Najeriya ga abokansa da ’yan Jari-hujja.

Wani yarfen kuma shi ne inda Ministan Labarai Lai Mohammed ya kira wani taron ’yan jarida inda ya zargi ’yan adawa ciki har da PDP da shirin tayar da tarzoma kafin zaben bana.

“Mun samu labaran sirri cewar Jam’iyyar PDP ta kammala shiri tsaf domin amfani da ’yan Boko Haram da ’yan bindiga dadi a Jihar Benuwai domin kashe mutane da dama kafin lokacin zaben. “Su dai ’yan adawa sun karaya ne, shi ya sa suke shirin tayar da yamutsi ta yadda zai kasance ba za a iya gudanar da zabe ba. Burinsu shi ne a kafa gwamnatin rikon kwarya,” inji shi.

Sai dai a martanin PDP ta ce Jam’iyyar APC ce ke bi-ta-da-kulli ga zaben.

Sauran ’yan takara irin su Hamza Al-Mustapha na Jam’iyyar PPN da Obadiah Mailafia na Jam’iyyar ADC, jam’iyyar da Cif Olusegun Obasanjo ya sanya wa albarkar a kwanakin baya da Oby Ezekwesili ta Jam’iyyar ACPN da Farfesa Kigsley Moghalu na Jam’iyyar YPP da Omoyele Sowore na Jam’iyyar AAC da Tope Kolade Fasua na ANRP da sauransu suna ta kokarin bayyana kudirorin su da abubuwan da za su aiwatar idan suka ci zabe.

Dokta Ezekwesili duk inda ta je tana kira ne ga ’yan Najeriya su yi watsi da APC da PDP, tana cewa jam’iyyun biyu ba su da bambanci.

A makon jiya ta aibata Shugaba Buhari da cewa ba ya da ilimin tattalin arziki, kuma ta bayyana hirar da Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo suka yi da Khadaria Ahmed a gidan talabijin na NTA a matsayin kasawa mai ban al’ajabi.

Kuma ta kushe dan takarar PDP, Atiku inda ta bayyana shi da dan Jari-Hujja da zai sayar da kasar nan ga kansa da abokansa. Ta ce idanhar shiga kasar Amurka da ya yi bayan shekara 12 wani babban abin alfahari ne ga Jam’iyyar PDP, to lallai akwai matsala a Najeriya.

Tsohon Shugaban Kasa Cif Obasanjowanda yake mara wad an takarar PDP Atiku Abubakar ne ya yi yarfe mafi muni a karshen makon jiya da farkon wannan mako, inda a wani taron manema labarai a gidansa a Jihar Ogun ya yi tofin Allah tsine ga Shugaba Buhari da Jam’iyyar APC da Hukumar INEC.

Ya yi kaca-kaca da Buhari kuma ya aibanta shi da mutumin da bai iya mulki ba, wanda ya mamaye gwamnati da ’yan uwansa, kuma ya bari mukarrabansa suna sama-da-fadi da dukiyar al’umma.

Don haka ya ce yana fatan ’yan Najeriya su yi watsi da Buhari su zabi Atiku.

Masoya Buhari sun mayar wa Obasanjo amsa inda suka ce idan maye ya manta to uwar ’ya ba ta manta ba.

Tsohon Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas, Alhaji Abubakar Tsab, ya yi wankan risga ga Cif Obasanjo a wata doguwar wasika da ya sake a shekaranjiya Laraba.

“Hakika Obasanjo ya raina hankalin ’yan Najeriya. In ban da rainin hankali yaya za a yi a ce kura ta ce da kare maye?” inji shi. Ya nuna matukar mamaki cewa Obasanjo ne zai fito ya kushe mulkin Shugaba Buhari, alhalin shi (Obasanjo) ya yi bakin mulki a shekarun 1999 zuwa 2007.

Abubakar Tsab ya ce ’yan Najeriya ba su taba ganin lalatacciyar gwamnati kamar ta Obasanjo ba, don haka ba ya da hurumin da zai kushe gwamnatin da ke ci a yanzu.

Sanata Bola Tinubu da Rotimi Amaechi sun ce ciwon tsufa ne ya kama Obasanjo don haka yake ta rafkanuwa. “In dai ba wanda ya samu motsi a kwakwalwarsa ba, ya ya za a yi Obasanjo ya ce ’yan Najeriya su zabi Atiku?” inji Tinubu.

“Obasanjo ne mutumin da rubuta littafi ya bayyana cewa a duk fadin Najeriya babu wanda ya ci amanar kasa kuma ya kwashe dukiyar al’umma kamar Atiku,” inji shi.

Amaechi ya bayyana Obasanjo a matsayin mutumin da ya rude.

“Obasanjo fa akwai lokacin da ya taba cewa Allah zai tsine masa idan ya goyi bayan Atiku ya zama Shugaban Kasa, to amma ga shi yau shi ne shugaban ’yan barandan siyasar Atiku. Ya kamata ’yan Najeriya su hankalta, tabbas Obasanjo yana tsoro ne idan Buhari ya sake cin zabe zai kai shi gaban kotu kuma za a daure shi,” inji Amaechi.

A yarfen Obasanjo ga INEC ya zargin shugabannin hukumar da kammala shiri tsaf domin taimaka wa Jam’iyyar APC ta yi magudi.

Sai dai Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakuba ya ce wannan batu shaci-fadi ne kawai.

A wani taro da yayi da shugabannin ’yan sanda, Farfesa Yakubu ya ce tabbas za su gudanar da zabe na gaskiya ba tare barin wata jam’iyya ta tafka magudi ba.

’Yan Najeriya sama da miliyan tamanin ne suka yi rajistar zabe, kuma ana sa ran miliyoyi daga cikinsu zasu fito su kada kuri’a. Sai dai yawancinsu a tsorace suke ganin yadda ’yan siyasa ke gudanar da kamfe dinsu.

Masana ilimin zaman takewa suna nuna rashin jin dadin a kan yadda ’yan siyasa ba sa bayanin abubuwan kirki sai dai zagin juna da yarfe.

A hira da yayi da Aminiya, Shugaban Tsangayar Halayyar Dan Adam (Sociology) a Jami’ar Abuja, Dokta Abubakar Kari, ya ce abubuwan da suke faruwa a yanzu ba sabon abu ba ne. “Siyasar Najeriya tun 1960 ta gaji haka,” inji shi.

“Yawancinsu suna dimaucewa idan lokacin zabe ya karato don haka suke tona asiri da kuma yin sharri ga junansu,” inji shi.

Game da ko akwai abin damuwa a kan subutar bakin da Buhari ya yi a Jihar Delta, sai ya ce, “Ko kadan ban damu ba; ai abin da Buhari ya yi zai iya faruwa ga kowa, musamman ganin yadda yake zuwa kamfe a jihohi biyu a kullum, baya  ga hidimar mulki.”

Game da kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na tuhumar Atiku cewa yana da hannu a durkushewar Bankin PHB, sai ya ce “Duk dai maganar siyasa ce kawai, ina da yakinin ba za su gufanar da shi gaban kotu ba a wannan lokaci.”

Dokta Kari ya yi kira ga ’yan siyasa su canja salon kamfe dinsu. “Ya kamata su daina yarfe wa juna, abin da ’yan Najeriya suke bukata shi ne su samu shugabannin da za su yi musu aiki. Don haka ina kira ga ’yan takara su bayyana wa mutane abubuwan da za su yi dalla-dalla,” inji shi.

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta