Zaben Bangladesh ya bar baya da kura
Firayiministar Bangladesh, Shaikha Hasina, wadda ke ikrarin samun nasara a zaben da jam’iyyun adawa suka kauracewa, ta ce za a iya sake sabon zabe ne idan ’yan adawar suka daina tashe-tashen hankula. Wannan zabe dai ya bar baya da kura, musamman ganin yadda kafafen yada labaran duniya ke bazawa.’Yan adawa sun kira yajin aiki na […]

Firayiministar Bangladesh, Shaikha Hasina, wadda ke ikrarin samun nasara a zaben da jam’iyyun adawa suka kauracewa, ta ce za a iya sake sabon zabe ne idan ’yan adawar suka daina tashe-tashen hankula. Wannan zabe dai ya bar baya da kura, musamman ganin yadda kafafen yada labaran duniya ke bazawa.
’Yan adawa sun kira yajin aiki na sa’o’i 48, al’amarin da ya haifar da tashe-tashen hankula, har aka kashe mutum bakwai, kuma aka haifar masakun kasar asarar Dala biliyan 22, baya ga cewa su ne kashin bayan tattalin arzikin kasar, domin su ne ke da kaso 80 cikin 100 na kayan da kasar ke fitarwa zuwa kasuwannin duniya.
Jam’iyyar Sheikha Hasina ta Awami League, ta mamaye kujerun majalisa da kashi biyu bisa uku, bayan da masu sa ido na kasashen duniya suka soki lamirin zaben, kuma ’yan adawa suka yi watsi da shi, musamman Jam’iyyar Khaleda Zia ta BNP. Kodayake babu wanda yake inkarin nasarar da jam’iyya mai mulki ta samu, tunda ba a yi takarar ko da rabin kujerun da suka yi saura ba.
“Za a iya sake zabe a kowane lokaci idan Jam’iyyar BNP ta zauna aka tatauna, amma dole ne su daina tayar da hankali,” inji Shekha Hasina, a lokacin da take jawabi a cikin furannin gidanta.
Mafi yawan shugaban Jam’iyyar BNP suna tsare a kurkuku, ita ma shugabar jam’iyyar Begum Khaleda Zia, ta ce an yi mata daurin talala a gidanta, al’amarin da gwamnati ta karyata.
Wani Farfesa, masanin kimiyyar siyasa, Ataur Rahman, da ke Jami’ar Dhaka, ya bayyana cewa wannan takaddamar rikiin siyasa da kasar ke fama da ita, za ta iya dakile bunkasar tattalin arzikin kasar.
kasar Amurka ta yi tur da wannan zabe na Bangladesh, inda ta ce bai yi nuni da bukatun al’ummar Bangladesh ba. Don haka t ayi kira kan a sake zabe.
Wani jami’in zabe da ba ya so a ambaci sunansa, ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa, yawan wadanda suka fito don kada kuri’a duk bai wuce kashi 40 cikin 100 ba. Ita kuwa kungiyar sa’ido ta EWG (Election Working Group), ta ce yawan wadanda suka yi zaben bai wuce kashi 30 cikin 100 ba. kungiyar Tarayyar Turai ta EU, wadda ke sayen kusan kashi 60 cikin 100 na kayayyakin da masakun Bangladesh suka saka, ta ki tura jami’an sa’ido