ZABEN BAYELSA: Ban ji dadin rashin fara zabe da wuri a mazabata ba – Jonathan

A yanzu haka tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kada kuri’arsa a rumfar zabe ta Unit 39 mazabar Ward 13 da ke Otuoke Karamar Hukumar Ogbia, jihar Bayelsa. Jonathan, ya bayyana rashin jin dadinsa game da rashin fara zabe da wuri a mazabarsa inda ya ce ya halarci rumfar zabe da misalin karfe 8:19 na […]

ZABEN BAYELSA: Ban ji dadin rashin fara zabe da wuri a mazabata ba – Jonathan

Jonathan a rumfar zabe

A yanzu haka tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kada kuri’arsa a rumfar zabe ta Unit 39 mazabar Ward 13 da ke Otuoke Karamar Hukumar Ogbia, jihar Bayelsa.

Jonathan, ya bayyana rashin jin dadinsa game da rashin fara zabe da wuri a mazabarsa inda ya ce ya halarci rumfar zabe da misalin karfe 8:19 na safe amma babu kayan gudanar da zabe don haka ya koma gida daga baya ya dawo don kada kuri’arsa bayan karfe 11.