Zaben Bayelsa: ’Yan sanda sun yi alkawarin samar da cikakken tsaro
Rundunar ‘yan Sandan jihar Bayelsa ta ce, za ta tabbatar da cikakken tsaro yayin zaben Gwamnan jihar da za a yi gobe Asabar. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Asnim Butswat, ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da Kamfanin Dillanci Labarai NAN yau Juma’a a Yenogoa babban birnin jihar. SP Asnim, ya kara […]
Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya Mohammed Adamu
Rundunar ‘yan Sandan jihar Bayelsa ta ce, za ta tabbatar da cikakken tsaro yayin zaben Gwamnan jihar da za a yi gobe Asabar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Asnim Butswat, ne ya bayyana hakan yayin da yake tattaunawa da Kamfanin Dillanci Labarai NAN yau Juma’a a Yenogoa babban birnin jihar.
SP Asnim, ya kara da cewa, a yanzu haka rundunar ta kammala duk shirinta na hanyoyin gudanar da zabe cikin lumana. Ya kuma bukacki ‘yan siyasar jihar da su kiyaye doka don taimakawa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukan su.