Zaben Buhari da El-Rufa’i alheri ne ga Jihar Kaduna – Sarkin Samari
Sarkin Samarin Masarautar Jama’a da ke Jihar Kaduna Alhaji Mudi Shafi’u Tahir ya ce zaben da aka yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i domin dorawa kan ayyukan raya kasa da suka faro ba karamin alheri ba ne ga al’ummar Jihar Kaduna da kasa baki daya. Sarkin Samarin ya […]
Sarkin Samarin Masarautar Jama’a da ke Jihar Kaduna Alhaji Mudi Shafi’u Tahir ya ce zaben da aka yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i domin dorawa kan ayyukan raya kasa da suka faro ba karamin alheri ba ne ga al’ummar Jihar Kaduna da kasa baki daya.
Sarkin Samarin ya kuma bayyana cewa tataburzar da aka yi ta yi kan Gwamna El-Rufa’i ya dauki Mataimakiya mace kuma Musulma da duk irin hasashe da hadarin da ake ganin hakan zai haifar yanzu ya zama tarihi, inda ya gode wa Allah kan yadda jama’ar Jihar Kaduna suka nuna wa duniya cewa ba za su bari a ci gaba da raba kansu da sunan addini ba.
“Duk da cewa Jam’iyyar PDP ce ta lashe mafi yawancin kananan hukumomin Kudancin Jihar Kaduna, ko ba komai irin ruwan kuri’un da Jam’iyyar APC ta samu ba a yankin a taba zaton samun irinsu ba wanda hakan ke nuna ci gaban da aka samu tunda ba kabila daya ko mabiya addini daya suka zabe shi a yankin ba,” inji shi.
Sarkin Samarin, wanda ya bayyana haka a tattaunawa da wakilin Aminiya a garin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jama’a, ya yi kira ga ’ya’yan jam’iyyun adawa su bai wa Gwamnan hadin kai domin ciyar da jihar gaba.
“Ba za mu ce a bar adawa ba amma idan za a yi, to a yi mai ma’ana kan abubuwan da za su farkar a kan ayyukan raya kasa ba adawar da ke nuna wani bangaranci ko yankin da mutum ya fito ko addininsa ko kabilarsa ba. Na yi imani irin manyan ayyukan da Gwamna El-Rufa’i ya faro ya shafi hatta kananan hukumomin da ba su zabe shi ba a shekarar 2015 kuma jawabin da ya yi bayan nasarar lashe zaben da ya yi ya nuna cewa a shirye yake ya tafi da duk mai kishi da kaunar ci gaban Jihar Kaduna ba tare da la’akari da addini ko kabila ko kuma yankin da mutum ya fito ba,” inji Sarkin Samarin Jama’a.