Zaben cike gurbi a Kogi: Siyasar kabilanci ta jefa APC a tsaka mai wuya

Ga dukkan alamu siyasar kabilanci da ke da matukar tasiri a Jihar Kogi ta jefa Jam’iyyar APC da ke kan gaba a zaben Gwamnan Jihar Kogi da aka faro a ranar 22 ga Nuwamba kuma ake sa ran kammalawa gobe a tsaka mai wuya.An bayyana Dan takarar Jam’iyyar APC marigayi Alhaji Abubakar Audu ya rasu […]

Zaben cike gurbi a Kogi: Siyasar kabilanci ta jefa APC a tsaka mai wuya

Ga dukkan alamu siyasar kabilanci da ke da matukar tasiri a Jihar Kogi ta jefa Jam’iyyar APC da ke kan gaba a zaben Gwamnan Jihar Kogi da aka faro a ranar 22 ga Nuwamba kuma ake sa ran kammalawa gobe a tsaka mai wuya.
An bayyana Dan takarar Jam’iyyar APC marigayi Alhaji Abubakar Audu ya rasu ne a daidai lokacin da Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ce ba a kamala zaben ba, sai dai kuma shi ne ya lashe mafi yawan kananan hukumomin jihar a sama da Gwamna Idris Wada.
Rasuwar ta Abubakar Audu ta daDa fito da yadda siyasar kabilanci ta yi katutu a zukatan al’ummar jihar musamman ’yan kabilar Igala masu rinjaye waDanda suke rike da kujerar Gwamnan Jihar tun dawowar mulkin farar hula, ko ma a ce tun kafa ta in aka cire waDanda ake turawa a zamanin mulkin soja.
Bayyana cewa ba a kammala zaben ba kafin rasuwar Abubakar Audu, saboda Hukumar INEC ta cewa a wasu rumfunan zabe 91 yawan waDanda suka jefa kuri’a sun haura waDanda suka yi rajista ne, ya sa ta soke zaben. Kuma Hukumar INEC ta umarci APC ta maye gurbin Dan takararta da ya rasu don ya samu shiga zaben cike-gibin da za a gudanar a gobe Asabar. Nan take Jam’iyyar APC ta maye gurbin marigayi Abubakar Audu da Alhaji Yahaya Bello wanda ya zo na biyu a zaben fid-da-gwani da APC ta gudanar a ranar 13 ga Agustan da ya gabata, kuma wanda ya fito daga kabilar Ibira, wadda ita ce kabila ta biyu mafi yawan jama’a a jihar.
Bayan APC ta mika sunan Yahaya Bello, kuma Kakakin Hukumar INEC Nick Dazang ya tabbatar da amsar sunansa daga APC a ranar Litinin da ta gabata, sai aka fara gudanar da zanga-zanga a wasu sassan yankin Igala. Sannan mataimakin marigayi Dan takarar James Faleke wanda uwar Jam’iyyar ta gayyata zuwa wani taron sasantawa kuma ta sake tabbatar masa da kujerar mataimakin Dan takarar Gwamna shi ma ya fice daga taron cikin fushi kan wannan mataki da jam’iyyar ta Dauka. Kuma ya yi alkawarin zai kalubalanci hakan a kotu.  Ya ce bai kamata Hukumar INEC ta bayyana cewa ba a kammala zaben ba, saboda waDanda aka tantance kuma suke da katin zabe na dindindin a rumfunan zabe 91 shi ne mutum dubu 25 – kasa da bambancin tazarar da APC ta ba PDP na kuri’a dubu 41. Don haka sai ya bukaci a bayyana shi a matsayin zababben Gwamna a cikin wasiku biyu da ya tura wa INEC da APC.
Rahotanni sun ce mutanen Kogi ta Yamma ne suke matsa wa Faleke cewa kada ya amince da zaben Bello, mutumin da bayanai suka ce shugabannin APC tare da goyon bayan wasu a fadar Shugaban kasa suka zabi ya rika wa APC tuta, saboda shi ya zo na biyu a zaben fid-da-gwani da Audu ya lashe.
Akwai kuma bayanan da suka nuna cewa shugabannin APC suna ganin bai dace ba Mohammed Audu Dan marigayi Abubakar Audu ya zama Dan takarar jam’iyyar ba, domin bai tsaya takara a zaben fid-da-gwani na jam’iyyar ba. “Shugabanni sun cimma matsaya cewa saboda Bello ne ya zo na biyu a bayan Audu a halattaccen zaben fid-da-gwani na jam’iyyar, maimakon jawo sabon rikici wajen gudanar da zaben fid-da-gwani, jam’iyyar ta zabi ta karkaDe sakamakon wanda Hukumar INEC ta halarta,” inji majiya mai karfi a hedkwatar APC.
Wani jigon APC ya faDi game da dalilin zaben Bello cewa:  “Shugabanninmu sun amince da cewa Faleke bako ne a siyasar jihar, saboda ya gudanar da mafi harkar siyasar ce a Legas. Suna jin ya fi dacewa ya fara koyo daga kasa kafin ya zamo Gwamna. Kuma sun amincewa zaben Bello zai tabbatar da gusawa da mulki a jihar tunda dai Ibira suna bayan Audu, don haka ba za zai zamo da wahala ba a inganta fahimtar juna a tsakanin Kogi ta Gabas da Kogi ta Tsakiya ba. Kuma kada ku manta Kogi ta Gabas dama ta samu kujerar Minista daga jihar.”
Ya kara da cewa wasu daga cikin rumfunan zabe 91 da aka soke zabensu suna Kogi ta Tsakiya ne, kuma zai fi zama mai sauki a shawo kan masu zab a yankin a samu kkuri’un da aka bukata don kayar da Gwamna Idris Wada na Jam’iyyar PDP. Ya ce shugabannin jam’iyyar sun ki Daukar Mohammed Audu ne bias lura da Sashi na 141 na Dokar Zabe, inda ya ce idan suka zabe shi Daukacin zaben baya ya haramta.
Sashin ya ce: “Kotun zabe ko kotu ta kowane dalili ba za ta bayyana cewa wani mutum ya ci zabe ba, a zaben da wancan mutum bai taka rawa a dukkan matakai na wancan zabe ba. “Muna son Audu amma ba za mu Dauki wannan babbar asara ba. Domin idan Wada da PDP suka je kotu za su samu nasara a kan Mohammed Audu,” inji shi.
Mista James Faleke, wanda ya ki amincewa da matsayin jam’iyyar na ya ci gaba da rike matsayin Mataimakin Dan takarar Gwamnan, kuma ya tsaya kai da fata cewa shi ne Dan takarar jam’iyyar, ya Dauki Mohammed Audu a matsayin Mataimakinsa a zaben cike gurbi na gobe.
Kuma da ta tabbata cewa Jam’iyyar APC tana nan kan bakanta cewa Yahaya Bello ta tsayar kuma ba sauyi, sai Falake ya shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja yana bukatar ta bayyana shi a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kogi. Kuma ya rubuta wa Hukumar INEC takarda cewa yana bukatar ta cire sunansa daga Mataimakin Bello.
A karar da lauyansa Wole Olanipekun, Falake wanda a yanzu haka Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Legas, ya ce da’awar hukumar zabe na cewa ba a kamala zaben ba, da kuma kasancewarsa Mataimakin ga Abubakar Audu ya wajaba a bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Lauyansa Olanipekun ya rubuta wa kotun cewa: “A doka da hankali, babu sabon Dan takara da zai gaji ko ya amfana da kuri’un da aka riga aka kaDa aka kirga tare da bayyana sakamakonsu daga INEC, kafin aa zabi wancan Dan takara da ake cewa shi jam’iyya ta tsayar. Kuma a Dauka cewa INEC tana ma da ’yancin ba da umarnin a gudanar da zaben cike gurbi, kuri’un da aka riga aka kaDa, aka kirga aka bayyana sakamakonsu ranar Asabar 25 ga Nuwamban bana, kuri’u ne na tikitin haDin gwiwa na Yarima Abubakar Audu da wanda muke karewa kamar yadda tsarin mulki ya nuna. Don haka babu sabon ko Dan takarar cike gurbi da zai kwace ko ya ci gajiya ko ya gaji waDancan kuri’u.”
Sakamakon matakin da Falake ya Dauka na kin kasancewa mataimaki ga Yahaya Bello a karashen zaben na gobe, tuni aka fara fafatawa neman maye shi.
Aminiya ta samu bayanai cewa manyan ’yan siyasa daga sassan jihar suna ta tururuwa zuwa gidan Bello don kamun kafa don samun hayewa kan kujerar. Duk da mun samu labarin burin Bello shi ne Mataimakinsa ya fito daga magoya bayan marigayi Audu, yanayin da siyasar jihar ke ciki ya sa shi fara tunanin Dauko Mataimakin kodai daga Yagba ta Gabas ko Yagba ta Yamma.
Kuma bayanai sun nuna cewa cikin waDanda ake sa ran su cike gurbin akwai tsohon Mukaddashin Gwamnan Jihar Clarence Olafemi da Mista Samuel Aro, wani tsohon Dan takarar Sanata a karkashin Jam’iyyar Accord.