…Zaben Ekiti alamar nasarar PDP ce a jihohin yamma –dan majen Yamma

dan Majen Jihohin Yamma, Alhaji Ibrahim Haruna da Jam’iyar PDP ta zaba a matsayin mai bayar da shawara a kan harkokin shari’a a karamar Hukumar Ibadan ta Arewa, Alhaji Ibrahim Haruna, ya ce, ba a taba yin zabe mai inganci a Najeriya kamar zaben da aka yi kwanan baya a Jihar Ekiti ba, inda ya […]

…Zaben Ekiti alamar nasarar PDP ce a jihohin yamma –dan majen Yamma
…Zaben Ekiti alamar nasarar PDP ce a jihohin yamma –dan majen Yamma

dan Majen Jihohin Yamma, Alhaji Ibrahim Haruna da Jam’iyar PDP ta zaba a matsayin mai bayar da shawara a kan harkokin shari’a a karamar Hukumar Ibadan ta Arewa, Alhaji Ibrahim Haruna, ya ce, ba a taba yin zabe mai inganci a Najeriya kamar zaben da aka yi kwanan baya a Jihar Ekiti ba, inda ya ce, “nasarar da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Mista Ayo Fayose, ya samu da ya lashe zaben, alama ce da ke nuna dunkulewar PDP a jihohi shida na Kudu maso Yammacin kasa, kuma alamar  dawowar mulkin PDP ne a wadannan jihohi a zaben shekara ta 2015.”
 A hirarsa da Aminiya, a Ibadan, Alhaji Ibrahim Haruna, ya ce, “mafi yawancin ‘yan siyasa a wannan sashe sun gaji da yin siyasar bangare daya mai akidar bambancin kabila da suke yi baya. Yanzu sun gano illar yin hakan shi ne yasa wasu mutane da suka yi fice a harkokin siyasa a Najeriya, suka hanzarta ficewa daga cikin jam’iyyar gado kaka da kakanni suka shigo cikin PDP da babu ruwanta da bambancin kabila, sai fafutukar neman hadin kan al’ummar Najeriya da ci gabansu.”
 Dangane da rade radin cewa, tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Otunba Christpher Adebayo Alao Akala, zai sake dawowa neman wannan mukami a zaben shekara ta 2015, sai ya kada baki ya ce, “tabbas gaskiya ne tsohon Gwamna Alao Akala, ya samu goyon bayan dubban mambobin jam’iyya daga sassa daban -daban na Jihar Oyo da suke so ya sake dawowa bisa wannan kujera, domin tserar da jihar daga halin kunci da APC ta jefa jama’a na tsawon shekaru uku da mulkin kama karya. Duk da yake akwai masu bukatar wannan kujera da suka fara nuna sha’awar wannan kujera, sai dai, fatanmu shi ne, ayi aiki da cancantar dan takara wanda muke kyautata zaton tsohon Gwamnan, ya riga ya tsallake  siradin zaben fitar da gwani a tsakaninshi da masu neman wannan matsayi a inuwar jam’iyar PDP a Jihar Oyo.”
Alhaji Ibrahim Haruna, wanda ya dade da kusantar tsohon Gwamna Adebayo Alao Akala, da suka yi ruguntsumin siyasa tare, ya ce, “duk da yake Alao Akala muke so ya samu lashe zaben fitar da gwani, sai dai, idan Allah bai kai shi ga nasara ba to, a shirye muke mu bayar da goyon baya ga dukkan wanda Allah ya dora a matsayin dan takarar gwamna, domin tabbatar da dunkulewar jam’iyarmu waje daya da muke fatan yin nasara a zabe mai gabatowa.”
Ya yi kira ga ‘yan Arewacin kasa mazauna jihar oyo suyi hakuri da irin takurawar da suka samu kansu a ciki a lokacin mulkin shekaru uku na kama karya da Gwamna Abiola Ajimobi, yake yi wanda ya janyo takurawar harkokin rayuwar jama’a a sassa daban-daban na jihar wanda ba a samu irin haka a zamanin da Gwamna Alao Akala yake mulki ba.