Zaben fid da gwani: Jam’iyyu sun yi yadda suke so saura ‘yan kasa

Zuwa yanzu dukan jam’iyyun siyasar kasar nan kusan 100 sun kammala zabubbukan fitar da ’yan takarar da za su tsaya musu a babban zaben 2019. Manyan jam’iyyun siyasar biyu, APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP, sun kare tarurrukansu ne da babban taro na kasa a ranar Asabar din da ta gabata a […]

Zaben fid da gwani: Jam’iyyu sun yi yadda suke so saura ‘yan kasa
Zaben fid da gwani: Jam’iyyu sun yi yadda suke so saura ‘yan kasa

Zuwa yanzu dukan jam’iyyun siyasar kasar nan kusan 100 sun kammala zabubbukan fitar da ’yan takarar da za su tsaya musu a babban zaben 2019. Manyan jam’iyyun siyasar biyu, APC mai mulki da babbar jam’iyyar adawa ta PDP, sun kare tarurrukansu ne da babban taro na kasa a ranar Asabar din da ta gabata a Abuja da Fatakwal babban birnin Jihar Ribas bi da bi.

A babban taron APC, Shugaban Kwamitin taron kuma Gwamnan Jihar Ekiti mai jiran gado Dokta Kayode Fayemi, ya tabbatar wa wakilan taron cewa a zabubbukan da aka gudanar a ranar Juma’a 28 ga Satumban da ya gabata ’ya’yan jam’iyyarsu miliyan 14 da dubu 842 da 72 suka zabi Shugaba Buhari ta hanyar ’Yar Tinke a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.

A can Fatakwal, bayan yadda iyayen jam’iyyar ta PDP suka dade suna kai-komo a kan samun maslaha tsakanin ’yan takarar jam’iyyar su 12 kan yadda wadansu za su hakura su janye, amma al’amarin ya ci tura, ala tilas jam’iyyar ta mika batun gaban wakilan taron su 3,274, suka yanke hukunci a zaben da aka yi zargin an yi wasa da kudi.

A karshe dai tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya zo na daya da kuri’a 1,532, sama da rabin kuri’un da aka kada. Shi kuma Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya zo na biyu da kuri’a 693, sai Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da ya zo na uku da kuri’a 317. Sanata Datti Baba-Ahmed mai Jami’ar Baze da ke Abuja, wanda a iya cewa shi ne al’majiri cikin dukan ’yan takarar neman shugabancin kasar a PDP ya zo na karshe da kuri’a 5.

Tuni dai wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa ta gindaya wa dukan jam’iyyun su tsayar da ’yan takara a ranar Lahadin da ya gabata ya cika, jam’iyyun sun kammala zabubbukan da suka yi matukar yamutsa hazo a harkokin siyasar kasar nan, kamar yadda aka saba samu a manyan jam’iyyu biyu da ake ba nasara, a duk lokacin da aka shigo kakar shekarar zabe irin wannan. A wannan karon APC da PDP ke cin karensu ba babbaka.

Masu lura da al’amurran da ke wakana a harkokin siyasar kasar nan sun yi hasashen cewa da wuya a kare lafiya a cikin zabubbukan fitar da ’yan takarar, musamman a cikin manyan jam’iyyun biyu, wato APC da PDP, kasancewar gwamnonin jihohi da shugabannin da sauran masu fada-a-ji a cikin jam’iyyun biyu, musamman inda adawar cikin gida ta zafafa, zabubbukan sun bar baya da kura fiye ma da yadda tarurruka da zabubbukan fitar da wakilan suka haifar, inda jihohi da dama suka kalubalanci yadda aka gudanar da su gaban kuliya.

Cikin irin wancan hali aka tafi tarurrukan fitar da gwanayen jam’iyyun wato ba tare da an warware wadancan tashin-tashina ba, ga kuma wasu sababbi da su sake kunno kai a cikin zabubbukan fitar da ’yan takarar, wadanda daga dukan alamu da su jam’iyyun za su shiga babban zaben. Kuma ga ’ya’yan jam’iyya da ba su gamsu da irin matakan da shugabannin suka dauka ba a zaman shawo kan matsalolin kuma sai su fara sauya sheka,kamar dai yadda aka saba gani a kasar nan a irin wannan lokaci.

Kamar dai yadda ta bayyana a cikin wadancan zabubbuka Jam’iyyar APC mai mulki, ita ta fi fama da rigingimun ko a mutu ko a yi rai, ta yadda duk da an tsai da zabubbukan fitar da ’yan takarar neman mukaman Gwamna a ranar 2  ga  Oktoban nan, amma zabubbukan ba su samu kammaluwa ba a ranar a jihohi irin su Zamfara da Enugu da Adamawa da Imo da Kwara, sai da suka kai cikin wannan mako.

A Jihar Zamfara ma inda Gwamnan Jihar ya shiga rikici da sauran ’yan takarar Gwamnan Jihar su takwas da suka hada da Mataimakinsa, Alhaji Ibrahim Mahammad Wakkala da tsohon Gwamnan Jihar, Alhaji Mahmud Aliyu Shinkafi da Ministan Tsaro Birgediya Janar Mansur Dan Ali (mai ritaya) da Sanata Kabiru Marafa, bisa tsai da Kwamishinan Kudi, Alhaji Mukhtar Shehu Idris da Gwamnan ya yi.

Bayan rushe dukan kwamitocin shugabancin Jam’iyyar APC, tun daga kan na mazabu zuwa na kananan hukumomi zuwa na jihar baki daya da Shugaban Jam’iyyar na Kasa Adams Oshiohmole ya yi a kan rikicin na Zamfara, amma rikicin sai da ya lashe rayukan mutum biyar. A Jihar Imo kuwa wadansu jiga-jigan APC ne da suka kafa kungiyar hadaka a kan yadda za su tunkari Gwamnan Jihar, Cif Rochas Okoracha da ya tsaya kai da fata a kan lallai sai mijin ’yarsa kuma Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Mista Uche Nwosu ne za a tsayar.

A babbar jam’iyyar adawa ta PDP ma an samu irin waccan sa-in-sa a jihohin Kano da Ogun da Gombe. Har yanzu a Jihar Kano ana ci gaba da takun-saka, bayan Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya nada surukinsa kuma tsohon Kwamishinan Ayyuka da Gidaje, Alhaji Abba Kabiru Yusuf a matsayin wanda zai yi wa PDP takarar Gwamnan Jihar. Nadin da shugaban PDP na jihar, Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa ya ce ba za ta sabu ba. Haka labarin yake a wadancan jihohi da na ambata a PDP.

Ko shakka babu yadda aka kasa samun yi wa ’ya’yan jam’iyya adalci a cikin zabubbukan fitar da gwanayen manyan jam’iyyun biyu, yana nuna wa ’yan kasa cewa idan har shugabanni da sauran masu fada-a-ji a cikin jam’iyyun biyu, za su yi wa junansu haka, to yaya za ta kasance idan aka zo babban zabe mai zuwa.

Yanzu ba abin da ya rage ga masu kada kuri’a wadanda za su zama alkalai kan zaben face su tashi tsaye da addu’o’i da kuma tabbatar da cewa a zabubbukan na 2019, sun zabi mutane nagari da suke da yakinin za su kamanta gaskiya da adalci, ta yadda burin da akasarin talakawan kasar nan suke da shi na yadda kasar nan da mutanenta za su fita daga mummunan halin tabarbarewar tattalin arzikin kasa da na tsaro da ma na zamantakewa ya cika.