Zaben gobe: A ci gaba da addu’ar Allah Ya sa a yi lafiya – Imam Aliyu
Limamin Masallacin Juma’a na ’Yan Doya da ke Jos fadar Jihar Filato, Imam Aliyu Aliyu Muhammad ya yi kira ga limamai da shugabannin addini su yi kokarin jawo hankalin al’umm a dukkan masallatai wajen ci gaba da yin addu’o’in Allah Ya sa a yi zaben gobe Asabar da wanda zai biyo bayansa nan da mako […]
Limamin Masallacin Juma’a na ’Yan Doya da ke Jos fadar Jihar Filato, Imam Aliyu Aliyu Muhammad ya yi kira ga limamai da shugabannin addini su yi kokarin jawo hankalin al’umm a dukkan masallatai wajen ci gaba da yin addu’o’in Allah Ya sa a yi zaben gobe Asabar da wanda zai biyo bayansa nan da mako biyu lafiya.
Malam Aliyu Aliyu Muhammad ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Jos, inda ya yi kira ga matasa kan su ji tsoron Allah su yi biyayya kada su bari a yi amfani da su wajen tayar da fitina a lokacin zaben.
“Ya kamata matasan Najeriya su kwantar da hankalinsu, a lokacin gudanar da zaben. Domin duk abin da babu kwanciyar hankali, ba za a samu nasara ba, amma duk abin da aka yi shi a cikin kwanciyar hankali za a samu nasara,” inji shi.
Hakazali ya yi kira ga al’ummar Najeriya kan su ji tsoron Allah su sani cewa wannan hali da suka samu kansu a ciki, ya faru ne sakamakon rashin rike amana da suke yi. Ya ce da sun rike amana da irin wadannan miyagun abubuwa ba su faru ba. Don haka su ji tsoron Allah su rike amana, shi ne zai kawo zaman lafiya da ci gaba a Najeriya.