Zaben Gwamna: Dan takarar PDP a Kano ya sha kaye a rumfar zabensa
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya lashe rumfar zaben abokin takararsa na jam’iyyar adawa ta PDP Injiniya Abba Kabir Yusuf. Rumfar zaben da ke unguwar Diso a karamar hukumar Gwale na bayyana sakamakon zaben rumfar kamar haka: Jam’iyyar APC ta dan takarar Gwamnan jihar mai ci ta samu kuri’u 172, yayin da abokin takararsa […]
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya lashe rumfar zaben abokin takararsa na jam’iyyar adawa ta PDP Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Rumfar zaben da ke unguwar Diso a karamar hukumar Gwale na bayyana sakamakon zaben rumfar kamar haka: Jam’iyyar APC ta dan takarar Gwamnan jihar mai ci ta samu kuri’u 172, yayin da abokin takararsa na PDP Abba Yusuf ya samu kuri’u 90.
Sai dai an samu rahoton fwasu matsalolin da aka fuskanta lokacin zaben yau Asabar, kamar satan akwatuna da sayan kuri’u da karancin shekarun yin zabe a wasu rumfanan zaben kananan hukumomi 44 na jihar.