Zaben Gwamna: Rundunar ’yan sandan Jihar Osun tana kara kyautata damararta
Rundunar ’yan sanda a Jihar Osun, tana kara shirye-shirye don yin kyakkyawar damara wajen tsayuwar daka kan kare lafiya da dukiyar jama’a, musamman a lokacin da za a gudanar da zaben gwamna da kananan hukumomi a lokuta daban-daban na watannin Mayu da Yunin bana. Kwamishinar ’yan sanda ta jihar, Uwargida Dorothy Gimba ce ta bayyana […]
????????????????????????????????????

Rundunar ’yan sanda a Jihar Osun, tana kara shirye-shirye don yin kyakkyawar damara wajen tsayuwar daka kan kare lafiya da dukiyar jama’a, musamman a lokacin da za a gudanar da zaben gwamna da kananan hukumomi a lokuta daban-daban na watannin Mayu da Yunin bana.
Kwamishinar ’yan sanda ta jihar, Uwargida Dorothy Gimba ce ta bayyana haka a wata hirarsu da Aminiya a ofishinta da ke Osogbo, inda ta yi nunin daga cikin shirye-shiryen, rundunar za ta yi kokarin gano dalilan da suka ko suke haifar da rikice-rikicen siyasa a lokutan zabe na baya, domin a sami matakan da za a dauka wajen magance aukuwar hakan a zabubbukan da ke biyowa. “Muna nan muna gano wuraren da ake ganin za a iya tayar da zaune-tsaye a lokutan wadannan zabubbuka, kuma muna yin duk abin da za mu iya don samo ingatattun bayanai na kulle-kullen da ake yi ko za a yi dangane da hakan. Da zarar mun fahimci haka, mukan yi wa jama’a, musamman shugabannin jam’iyyun siyasa, bayanai a game da dokar kasa don su fahimta, lamarin da zai nuna in mutum ya karya dokar kasa, ba zai zargi kowa ba sai kansa, idan an hukunta shi”. Inji ta.
Dangane da yakin neman zabe, ta ce lallai jam’iyyu su nemi izni domin a tantance, ta yadda jam’iyu daban-daban ba za su hadu a rana daya kuma a gari daya, ko yin taro a kusa da juna ba, ta yadda za a sami natsuwa da zama lafiya.
Kwamishinar ta bayyana cewa ta tattauna da sauran mazauna jihar, musamman ’yan Arewa kan irin wayar da kan jama’a da rundunarta ke yi domin samun zama lafiya da kwanciyar hankali. Haka nan ta zauna da Fulani makiyaya, wadanda su ma ta yi musu bayanan irin gudunmawar da za su bayar na kyautata dangantaka tsakaninsu da manoma da taimakawa wajen magance batagari, wadanda yawanci suke kulla makirce-makircensu a daji.
Dangane da irin matsaloli da nasarori da rundunar ta samu a cikin watanni 11 da fara aikinta a jihar, Uwargida Dorothy ta ce, “Daga cikin manyan matsalolin da na fara fuskanta a lokacin da na kama aiki shi ne yawan aukuwar fashi da makami, musamman a kan hanyar Ile-Ife zuwa Ibadan da wanda ake yi a cikin manyan garuruwa. Mun zauna da manyan jami’aina, muka bullo da dabarun dakile wannan sha’ani, lamarin da ya taimaka mana wajen fatattakar ’yan fashi daga cikin Jihar Osun, wadda take babbar nasara gare mu, kuma ba wai mun yi sanyi ne a kan haka ba. Rikice-rikice a tsakanin al’ummomi da na sarautun gargajiya da na siyasa, musamman a garuruwan Ede da Oba-Ile da Oba-Oke, wadanda suka haifar da kone-konen kadarori da rasa rayuka, yanzu, cikin godiya ga Allah, mun shawo kan su da muka gano bakin zaren, bayan zaman da muka yi tare da sarakuna da dattijan gari da kuma matasa.” Inji ta.
Ta ce zuwa karshen watan jiya, rundunar ta gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar su 90 gaban alkalan kotuna, kuma akwai guda 99 da ke gaban alkalai.
An kama mutum 156 da ake zargi da fashi da makami da bindigogi 45 da harsasai 52. Haka kuma an kama mutum 78 da zargin yin fyade da mutum 26 da zargin kisan kai da mutum daya da zargin satar mutane da mutane 2 da aka ceto daga hannun wadanda suka sace su domin yin garkuwa da su da motoci 62 da babura 64.