Zaben Gwamnan Adamawa: Fintiri zai fafata da Jibrilla

Mukaddashin Gwamnan Jihar Adamawa Alhaji Ahmadu Fintiri wanda ya lashe zaben share fage na Jam’iyyar PDP a ranar Asabar da ta gabata zai fafata da Sanata Mohammed Jibrilla da ya lashe zaben share fage na Jam’iyyar APC a zaben Gwamnan Jihar da za a gudanar ranar 11 ga Oktoba mai zuwa.Ahmadu Fintiri, ya doke abokan […]

Zaben Gwamnan Adamawa: Fintiri zai fafata da Jibrilla
Zaben Gwamnan Adamawa: Fintiri zai fafata da Jibrilla

Mukaddashin Gwamnan Jihar Adamawa Alhaji Ahmadu Fintiri wanda ya lashe zaben share fage na Jam’iyyar PDP a ranar Asabar da ta gabata zai fafata da Sanata Mohammed Jibrilla da ya lashe zaben share fage na Jam’iyyar APC a zaben Gwamnan Jihar da za a gudanar ranar 11 ga Oktoba mai zuwa.
Ahmadu Fintiri, ya doke abokan takararsa ne a fafatawa mai zafi da ta kai kusan wayewar garin Lahadi, inda ya samu kuri’a 624, yayin da Dokta Ahmed Mohammed Modibbo ya zo na biyu da kuri’a 197.
Tsohon Gwamnan Jihar Legas Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya samu kuri’a 54, sai Umar Ardo da dan Majalisar Jihar, Jerry Kumdiisi, suka samu kuri’a tara da biyar.
Shugaban kwamitin zaben tsohon Shugaban Majalisar Tarayya Dimeji Bankole ne ya bayyana sakamakon zaben da karfe 4:03 na safiyar Lahadi.
An sa ran Fintiri ya lashe zaben bayan da ’yan takara takwas da suka janye suka goya masa baya. ’Yan takarar su ne Malam Nuhu Ribadu da Awwal Tukur da Idi Hong da Aliyu Kama da Markus Gundiri da Andrawus Sawa da Halilu Girie da kuma James Barka, wadanda suka ce sun amince su mara wa Fintiri baya ne saboda ya amince ba zai tsaya takarar share fage a zaben Gwamna da za a gudanar a Fabrairun 2015 ba.
Shi kuwa Sanat Jibrilla ya lashe zaben share fagen Jam’iyyar APC ne a washegari Lahadi, inda ya samu kuri’a 2,718 ya kayar da babban mai kalubalantarsa Ibrahim Mijinyawa, wanda ya samu kuri’a 2,268, kamar yadda shugaban zaben Talba Abari, ya sanar a sakatariyar jam’iyyar.
Boss Mustapha, ya zo na uku da kuri’a 515, yayin da Sanata Ahmed Barata da ke wakiltar Adamawa ta Kudu ya samu kuri’a 452, sai Yakubu Tsalla da Emmanuel Bello da suka samu kuri’a 147 da kuri’a 50 a jere.