Zaben Gwamnan Gombe: Kotu ta ba APC damar amfani da na’urar tantance kuri’a

Kotun Sauraron karar Zaben Gwamna a Jihar Gombe ta ba Jam’iyyar APC da ke kalubalantar zaben Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo na Jam’iyyar PDP damar ta kawo na’urar tantance kuri’a don tantance kuri’un da aka jefa a lokacin zaben da ya gabata. Alkalin Kotun Mai shari’a Mathew Adewara ne ya ba da wannan dama a ranar […]

Zaben Gwamnan Gombe: Kotu ta ba APC damar amfani da na’urar tantance kuri’a
Zaben Gwamnan Gombe: Kotu ta ba APC damar amfani da na’urar tantance kuri’a

Kotun Sauraron karar Zaben Gwamna a Jihar Gombe ta ba Jam’iyyar APC da ke kalubalantar zaben Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo na Jam’iyyar PDP damar ta kawo na’urar tantance kuri’a don tantance kuri’un da aka jefa a lokacin zaben da ya gabata.

Alkalin Kotun Mai shari’a Mathew Adewara ne ya ba da wannan dama a ranar Talatar da ta gabata. Jam’iyyar APC ta nemi kotunn ta ba ta damar don duba kayayyakin zabe da kuma kawo na’urar tantance kuri’a don tabbatar da sahihancin kuri’un da aka kada.
Da yake maida martani kan hukuncin Lauya mai kare wanda ake karar wato Gwamna Ibrahim dankwambo, Ibrahim Isiaku (SAN) ya ce a matsayinsa na lauya zai bi umarnin da kotun ta bayar na kawo na’urar.
Lauyan Jam’iyyar APC, Mista Ayola Ajayi, cewa ya yi ya ji dadi kan hukuncin da kotun ta yanke na ba su damar kawo na’urar, sai ya ce, “Ba ma jin cewa Hukumar INEC za ta nuna bangaranci a wannan karar, muna kyautata zaton ta zama mai cin gashin kanta tunda kotun ta nuna haka, kuma muna sa ran cewa INEC za ta ba mu hadin kai wajen samar wa dukkan bangarorin takardun da suke bukata ba kawai ga mai kara kadai ba.”
Shi kuwa lauyan INEC, Mista Hassan M. Liman (SAN) cewa ya yi ba da dama a shiga shafin intanet na hukumar don ganin yadda tantance yadda masu kada kuri’a suka jefa kuri’arsu ya saba wa doka kuma kotun ta amince da hakan.
Ya ce abin da kotun ta amince da shi, shi ne masu kara za su kawo na’urar da za ta tantance kuri’un da aka jefa ne kadai ba za a ba su izinin shiga yanar gizo na hukumar zaben ba domin yin hakan zai iya fallasa sirrin wadanda suka jefa kuri’ar.
Kotun ta dage zaman sauraron karar zuwa ranar 4 ga Yuli, inda za a fara sauraron karar gadan-gadan a ranar Litinin 6 ga Yuli.