Zaben Gwamnan Kogi: An fara zaben fidda gwani na PDP

A yau Talata an fara zaben fidda gwani na neman takarar Gwamnan jihar Kogi a jam’iyyar adawa ta PDP, za dai a gudanar da babban zaben Gwamnan jihar ne a ranar 16 ga Nuwamba 2019. An fara gudanar da zaben fidda gwanin ne a yammacin yau da misalin karfe 6:50 a filin wasa na  Confluence […]

Zaben Gwamnan Kogi: An fara zaben fidda gwani na PDP

A yau Talata an fara zaben fidda gwani na neman takarar Gwamnan jihar Kogi a jam’iyyar adawa ta PDP, za dai a gudanar da babban zaben Gwamnan jihar ne a ranar 16 ga Nuwamba 2019.

An fara gudanar da zaben fidda gwanin ne a yammacin yau da misalin karfe 6:50 a filin wasa na  Confluence Stadium, da ke Lokoja babban birnin jihar.

Shugaban Kwamitin zaben fidda gwani na PDP, Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri, ya ce a yanzu haka an tantance wakilan da ke zabo ‘yan takara (Delegates) dubu 2,388 cikin adadin dubu 2,511 daga Kananan Hukumomi 21 na jihar.

Shugaban Kwamitin ya ce ‘yan takarar 13 ne ke neman tsayawa takarar zaben kuma ba bu wani dan takarar da yake da niyyar janye wa.