Zaben Gwamnan Kogi, Bayelsa: A yau za a rufe karbar katin zabe

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kammala tantance jam’iyyu 68 don yin zaben Gwamna na ranar 16 ga Nuwamba 2019 a jihohin Kogi da Bayelsa. Hukumar INEC ta fitar da jadawalin jam’iyyun da zasu fafata a zaben 2019, wanda ta ce jami’iyyu 23 ne za su yi takarar zaben Gwamna a jihohin […]

Zaben Gwamnan Kogi, Bayelsa: A yau za a rufe karbar katin zabe

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kammala tantance jam’iyyu 68 don yin zaben Gwamna na ranar 16 ga Nuwamba 2019 a jihohin Kogi da Bayelsa.

Hukumar INEC ta fitar da jadawalin jam’iyyun da zasu fafata a zaben 2019, wanda ta ce jami’iyyu 23 ne za su yi takarar zaben Gwamna a jihohin biyu.

A ci gaba da shirin gudanar da zaben jihohin Kogi da Bayelsa inda ake ci gaba da raba katin zabe kuwa, hukumar INEC ta sanar da cewa a yau Litinin 30 ga Satumba 2019 za a rufe karbar katin zaben da ake yi a jihohin.