Zaben Gwamnan Nasarawa: Ana Zanga-zanga a Kotun Daukaka Kara

Al’ummar Nasarawa sun yi dafifi a kotun daukaka kara da ke shirin yanke hukunci kan kwace kujerer gwamnan jihar

Zaben Gwamnan Nasarawa: Ana Zanga-zanga a Kotun Daukaka Kara

A safiyar Alhamis din nan Kotun Daukaka Kara ta Tarayya taf fara zama domin yanke hukunci kan zaben Gwamnan Jihar Nasarawa, kan soke nasarar Gwamna Abdullahi Sule.

A halin da ake ciki al’ummar jihar ta yi cikar kwari tare da zanga-zana a kusa da kotun da ke zamanta a Abuja kan karar da Gwamna Abdullahi Sule na Jam’iyyar APC ya daukaka.

Hakan kuwa na zuwa ne washegarin zanga-zangar da magoya bayan Jam’iyyar NNPP suka gudanar a Jihar Kano kan tufka da warwara da aka samu a kundin hukuncin kotun daukaka karar da ta kwace kujerar Gwamna Abba Kabir Yusuf, amma kuma kundin hukuncin ya nuna ta tabbatar masa da kujerar tasa.

A Jihar Nasarawa dai Abdullahi Sule ya daukaka kara ne bayan kotun sauraron korafin zaben gwamann jihar, ta kwace kujerarsa ta ba wa babban abokin hamayyansa, David Ombugadu na jam’iyyar PDP.

Ombugadu ya garzaya kotu ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Adullahhi Sule na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u 347,209, Ombugadu na biyu kuma ya zo na biyu da kuri’u 283,016.

Amma a zaman kotun shari’ar zaben na ranar 2 ga Oktoba, ta soke zaben Abdullahi Sule tare da ayya Ombugadu a matsayin halastaccen zababben Gwamnan Jihar Nasarawa.

Amma Gwamma Abduullahi Sule, ta hannun lauyansa, Wole Olanipekun (SAN), ya daukaka kara yana nema Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta soke hukuncin farkon ta tabbatar da nasararsa.

A martanin lauyan PDP da Ombugani, Kanu Agabi, ya bukaci kotun daukaka karar ta kori bukatar Abdullahi Sule, domin kotun sauraron karar zaben ta rika ta yi duk abin da ya kamata wajen bin diddigin karar da suka shigar kuma ta tabbatar da nasarar Ombugadu.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta