Kotun Koli ta tabbatar da Kawun Davido a kujerar Gwamnan Osun
Kotun ta kori karar da tsohon Gwamna, Oetola da ke kalubalantar cancantar Adeleke na tsayawa takara a zaben.
Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a zaben Gwamnan Jihar Osun da aka gudanar a 2022.
Kotun Kolin ta kuma yi watsi da karar da tsohon Gwamna, Adegboega Oetola na Jam’iyyar APC ya shigar na kalubalantar cancantar Adeleke na tsayawa takara a zaben.
- Hajj 2023: Kamfanonin jirage da NAHCON sun daidaita kan jigilar maniyyata
- Jirgin ruwa ya nutse da mutum 20 a Sakkwato
Ta kuma caccaki Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Osun da ta ki amfani da hukuncinta na farko kan halaccin taakarar Adeleke.
Adekele kawu ne ga fitaccen mawakin Najeriya, Davido, wanda kuma ya yi a fadi-tashi tun lokacin yakin neman zaben kawun nasa.
Ko a makon jiya mawakin ya addu’ar samun nasara ga kawun nasa, wanda wasu ke wa lakabi da gwamnan mai rawa.