Zaben Gwamnan Osun: Kotun Koli za ta yanke hukunci ranar Talata

Koun Koli a sanya Talata 16 ga waan Mayu da muke ciki a matsayin ranar da za a yanke hukunci kan zaben gwamnan Jihar Osun.

Zaben Gwamnan Osun: Kotun Koli za ta yanke hukunci ranar Talata

Kotun Koli a sanya Talata 16 ga watan Mayu da muke ciki a matsayin ranar yanke hukunci kan zaben gwamnan Jihar Osun.

Alkalai biyar na kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a John Okoro sun sanya ranar ne bayan bangarorin da ke shari’a da juna sun karbi bayanan juna.

Gwamna Ademola Adeleke na Jam’iyyar PPD ya daukaka kara zuwa Kotun Koli ne bayan Kotun Daukaka Kara ta soke zaben sa, ta ayyana tsohon gwamnan Adegboyega Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar ranr 16 ga watan Yuni, 2022.

Alkalan kotun daukaka kara sun tabbatar da nasarar Oyetola na APC, wanda ya zo na biyu a zaben ne, bisa hujjar aringizon kuri’un da Adeleke ya samu a zaben.

Bayan soke kuri’un da aka yi aringizo, alkalai uku da suka saurari shari’ar suka yi ittifakin cewa Oyetola ne ya yi nasara a zaben.

Amma a karar da bangaren Adeleke ya daukaka zuwa Kotun Koli, ya bayyana cewa alkalan sun ti kuskuren yanke hukunci cewa an yi aringizon kuri’u a zaben.

Sun bayyana cewa dole sai Oyetola da APC sun tabbatar da hujjoji cewa an yi aringizon kuri’a.