Zaben Gwamnan Oyo: Kotu ta yanke hukunci mai rikitarwa
Kotun Koli za a je domin warware matsalar – Barista Surajo Danbaba A ranar Litinin da ta gabata ce magoya bayan jam’iyun PDP da APC da lauyoyinsu a Jihar Oyo suka shiga cikin zullumi kan hukunci mai rikitarwa da Kotun Daukaka Kara ta Ibadan ta yanke, inda ta soke hukuncin kotun sauraron karar zabe ta […]
- Kotun Koli za a je domin warware matsalar – Barista Surajo Danbaba
A ranar Litinin da ta gabata ce magoya bayan jam’iyun PDP da APC da lauyoyinsu a Jihar Oyo suka shiga cikin zullumi kan hukunci mai rikitarwa da Kotun Daukaka Kara ta Ibadan ta yanke, inda ta soke hukuncin kotun sauraron karar zabe ta jihar kan zaben Gwamna a tsakanin Gwamna Seyi Makinde na PDP da Mista Adebayo Adelabu na APC.
Kotun Daukaka Karar ba ta yanke hukunci a kan ainihin karar da dan takarar na APC Adebayo Adelabu ya shigar a gabanta ba inda yake neman ta soke zaben Gwamna na ranar 9 ga Maris da ya gabata wanda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da kotun sauraron karar zabe ta jihar suka tabbatar da Injiniya Seyi Makinde na PDP ne ya yi nasara.
Kotun Daukaka Karar da Mai shari’a Abubakar Yahaya, ya shugabanta ta yanke hukuncin cewa an yi rashin adalci a zaman kotun sauraron karar zabe a dalilin kasa la’akari da takardun da aka gabatar mata a matsayin shaida da masu kara suka shigar gabanta. Saboda haka Kotun Daukaka Karar ta ce, babu lokacin da za ta bayar da umarnin sake komawa ga kotun sauraron karar domin sake yin wannan shari’a domin wa’adin kwana 180 na waiwayar zaben ya riga ya wuce.
Aminiya ta lura cewa, bayan zartar da wannan hukunci mai rikitarwa ne dimbin magoya bayan jam’iyun na PDP da APC da lauyoyinsu suka rika fitowa daga cikin zauren kotun kowane da fuska a murtuke domin ba a yanke hukuncin da kowane bangare ya sa ran za a yi ba. Ita dai kotun ta ki bayar da umarnin soke zaben Gwamnan kuma ta ki bayar da umarnin sake yin sabon zabe kuma ta ki bayar da umarnin sake sauraron karar wanda hakan ne ya rikirtar da magoya bayan jam’iyun biyu da suka rika kebewa waje daya suna tattaunawa a kan wannan batu.
Dangane da wannan hukunci mai rikitarwa Aminiya ta tuntubi wani lauya Barista Surajo Danbaba wanda ya ce, “Kotun Daukaka Kara ta fara duba yadda kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke hukuncinta ne inda ta ce kotun ba ta yi adalci wajen yanke hukuncinta cewa Injiniya Seyi Makinde na PDP ne ya yi nasara ba. Saboda haka sai Kotun Daukaka Karar ta jingine wannan hukunci waje daya domin kotun ba ta bayar da damar sauraron bukatu hudu da masu daukaka kara suka nemi a biya musu ba.
Wannan yana nufin cewa, Kotun Daukaka Karar ta amince da wannan kara da Adebayo Adelabu na APC ya shigar a gabanta amma ba ta biya masa bukatu hudu da ya nemi a yi ba. Bukatun sun hada da soke zaben da sake sabon zabe.
Barista Surajo Danbaba ya ce, “Kotun Koli za a je domin warware matsalar domin yanzu haka muna jiran samun takardar sakamakon hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta zartar ne domin daukar mataki na gaba. An yi mana alkawarin samun wannan kwafin takarda ce a cikin wannan mako da bangarorin biyu za su daukaka kara da kewaye daukaka kara ‘Appeal and cross Appeal’ a Kotun Koli.”
Da yake yin watsi da batutuwan da ake yadawa cewa, hukuncin yana nufin sake zabe a wasu kananan hukumomin jihar ya ce, “Ko kusa ba haka ba ne domin Gwamna da ke kan karaga yana da damar daukaka kara zuwa Kotun Koli ba kamar wakilan majalisar dokoki da shari’arsu ta tsaya a Kotun Daukaka Kara ba.”