Zaben Gwamnan Zamfara: Mata na sayar da kuri’arsu a rumfar zabe

Rahotanni daga wata rumfar zabe a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara na bayyana wata mata da ake kira Hajiya an gano ta tana sayan kuri’ar masu zaben ‘yan takarar Gwamna da ‘yan majalisar dokoki a rumfar zaben da ake yi yau Asabar. Rumfar zaben dai, na hanyar Banaga Abubakar Chika, a wajen aka gano […]

Zaben Gwamnan Zamfara: Mata na sayar da kuri’arsu a rumfar zabe

Rahotanni daga wata rumfar zabe a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara na bayyana wata mata da ake kira Hajiya an gano ta tana sayan kuri’ar masu zaben ‘yan takarar Gwamna da ‘yan majalisar dokoki a rumfar zaben da ake yi yau Asabar.

Rumfar zaben dai, na hanyar Banaga Abubakar Chika, a wajen aka gano Hajiyar na rabar da lamba ga masu kada kuri’a .

An rubuta lambobi a jikin takardu, wanda ke nuna alamar idan an zabi wanda ake bukata sai a zo wurinta ta biya kudin kada kuri’ar da mai zabe ta yi a cikin wani gida.

Wakilinmu da ya ziyarci inda ake karbar kudin ya tarar da sama da mata 50 da suka yi zabe suna jiran a biya su kudaden da aka shirya biyan su.