Zaben Jamhuriyar Tsakiyar Afirka
A ranar 30 ga watan jiya ne aka gudanar da zaben shugaban kasa da kuma na ’yan majalisar dokoki a kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka. Zaben ya kara karfafa kyakkyawan fatan da ake da shi na samun zaman lafiya a kasar da ta fada rikicin kabilanci da na addini a ’yan shekarun nan. Kodayake, an ta […]
A ranar 30 ga watan jiya ne aka gudanar da zaben shugaban kasa da kuma na ’yan majalisar dokoki a kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka. Zaben ya kara karfafa kyakkyawan fatan da ake da shi na samun zaman lafiya a kasar da ta fada rikicin kabilanci da na addini a ’yan shekarun nan. Kodayake, an ta dage zabukan a lokutan baya.
’Yan takara 30 ne suka yi takarar neman shugabancin kasar, yayin da mutum 1,800 suka yi takarar kujerun majalisar dokokin kasar, kasar da a baya sojoji suke yawan juyin mulki. Fiye da mutum miliyan daya da dubu 800 ne suka kaka kuri’u rumfunar zabe guda 500 a fadin kasar, wadda Shugabar Rikon kwarya Catherine Samba-Panza take jan ragama tun watan Mayun shekarar 2014. Yadda jama’a suka fito kwanso da kwarkwatansu yana nuni da cewa sun fara mantawa da bambance- bambance, kuma sun amince za su zauna tare cikin lumana.
kasar wadda rikici ya daidaita tun watan Maris din shekarar 2013 a lokacin da kungiyar Gwagwarmayan Musulmi ta Seleka ta hanbarar da Shugaba François Bozizé. A lokacin da jagoran Seleka ya sauka daga mulki bayan matsin lambar daga kasashen duniya a watan Janairun 2014, sai kungiyar Kiristoci ta anti-Balaka suka fara daukar fansa a kan Musulmi. Rikici tsakanin Musulmi da Kiristoci ya ci gaba, inda ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum miliyan guda da kuma tilasta wa wasu da dama kaurace wa muhallinsu.
Gabanin gudanar da zaben, an fara yin zaben jin ra’ayin jama’a ne a ranar 13 ga watan jiyan, wadda ta zaman zakaran gwajin dafi, amma sai dai an samu rikice-rikice lokacin gudanar da hakan. Kodayake, lokacin babban zaben ba a samu rikici ba, wanda hakan ya sa ake ganin cewa akwai kyakkyawan fatan kasar za ta samu zaman lafiya mai dorewa bayan kwashe shekaru masu yawa ana zubar da jini.
Sakamakon farko na zaben shugaban kasar ya nuna cewa tsohon Firaministan kasar Faustin Archange Touadera shi ne yake kan gaba, yayin da shi ma wani tsohon Firaministan Anicet Georges Dologuele yake biye da shi. Kodayake, bayan an kidaya akalla kuri’u kashi 40 cikin 100, 20 cikin 30 na ’yan takarar sun bukaci dakatar da ci gaba da kidayawan bisa zargin almundahana. Har ila yau, za a kwashe lokaci ba tare da an bayyana sakamakon ba, hakan yana nuni da cewa zaben sai ya kai zagaye na biyu musamman idan aka yi la’akari da yawan ’yan takarar da ke takara a cikinsa. Za dai a gudanar da zagaye na biyu ne a ranar 31 ga watan nan.
Majalisar dinkin Duniya ta bayyana cewa zaben ya gudana ba tare da rikici ba. Kuma ta ce babbar nasara ce duk da cewa an fara zaben a makare. Tsohon Firaministan kasar Senegal wanda kuma shi ne Jagoran Masu Sanya Ido daga kungiyar Tarayya Afirka, Souleymane Ndiaye, ya bayyana cewa zaben an gudanar da shi cikin ’yanci. “ ’Yan takarar da suke korafi sun samu kuri’u da ba su wuce kashi guda cikin 100 wannan ne ya sa su korafi,” inji shi, jim kadan bayan ya dawo daga Bangui, babban birnin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka .
Zaben ya bai wa kasar damar kawo karshen rikicin addini, ta kuma bunkasa tattalin arzikinta da karfafa dimukradiyya a kasar da take cikin sawun kasashe matalauta na duniya. Har ila yau, wannan babbar dama ce da za ta taimaka wajen samun sulhu tsakanin bangarorin da ke fada da juna. Wannan ya sa muke kira ga wadanda suke ganin ba a yi musu daidai ba da su nufi kotu ko kuma su bi hanyoyin da doka ta tanada don warware matsalaloli, amma yana kyau su kauce wa tada zaune tsaye. Yakamata su yi koyi da sauran kasashen Afirka kamar Najeriya, Kwaddibuwa da Tanzaniya da kuma Burkina Faso, an gudanar da zabuka a wadannan kasashe kuma wadanda suka sha kayi sun amsa shan kayin duk da cewa akwai wasu ’yan matsaloli lokacin zabukan.
Jama’ar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka sun dade cikin wahala, kuma kasar ba ta samun sabbin masu zuba jari daga kasashen ketare lokaci mai tsawo. Wannan ya sa ya zama wajibi zaben ya kawo sahihin sauyi. Yana da muhimmanci duka ’yan takaran su taimaka wajen lalubo hanyoyin warware manyan kalubalen kasar.
Duk wanda ya lashe zaben a karshe, zai gaji kalubale masu yawa. Sabuwar gwamnati za ta fuskanci jan aikin karbe makamai daga hannun jama’a da kuma aikin dawo da tsofaffin masu dauke da makamai cikin al’umma da sauransu.