…‘Zaben Jonathan ya jefa mu a rikici a shekarar 2011’

Fiye da mutum 500 da rikicin bayan zaben shekarar 2011 ya shafa a Jihar Gombe wadanda suka yi asarar gidaje da dukiyoyinsu suka fito suka yi gangami a bakin Sakatariyar Jam’iyyar PDP don koka wa Gwamnatin Tarayya kan rashin ba su diyyar da aka yi musu alkawari. Mutanen sun bayyana cewa an yi musu alkawarin […]

…‘Zaben Jonathan ya jefa mu a rikici a shekarar 2011’
…‘Zaben Jonathan ya jefa mu a rikici a shekarar 2011’

Fiye da mutum 500 da rikicin bayan zaben shekarar 2011 ya shafa a Jihar Gombe wadanda suka yi asarar gidaje da dukiyoyinsu suka fito suka yi gangami a bakin Sakatariyar Jam’iyyar PDP don koka wa Gwamnatin Tarayya kan rashin ba su diyyar da aka yi musu alkawari.

Mutanen sun bayyana cewa an yi musu alkawarin za a biya su diyya tun a wancan lokaci amma ga shi har zabe ya sake zagayowa ba a biya su komai ba, inda suka ce idan ba a biya su ba, ba za su zabi PDP a zaben da ke tafe ba.
Mista Julius Joseph, wanda shi ne jagoran mutanen da rikicin bayan zaben ya shafa a Jihar Gombe ya ce sun yi mamanki kan yadda aka ki biyansu diyyar domin duk Najeriya a jihar ne aka fara rikicin bayan zaben inda a karamar Hukumar Funakaye aka fasa motar hukumar zabe kuma duk wata biyayya sun yi don a biya su amma har yanzu shiru.
Mista Julius Joseph, ya ce Gwamna dankwambo ya ce musu an ba shi tabbacin za a biya su tuntuni amma har yanzu an ce idan Gwamnan ya bi sawu sai a ce masa babu kudi.
Shugaban ya ce me ya sa ’yan majalisunsu na dattawa da na taryya da Minista da aka ce ’yan gaban goshin Shugaban kasa ne, ba su bi batun ba ko ba su da amfani ne don ba su abin ya
shafa ba?
Ya ce tun shekara biyu da suka wuce aka biya jihohi tara diyyar, Kaduna ma kwanan nan aka ware Naira biliyan uku za a biya jama’a, amma su a Gombe babu maganar za a biya su. “Rashin biyan mu ya sa mun gane cewa ana nuna mana wariya an cire Gombe daga Najeriya don haka kamar yadda muka zabi PDP ta ci, mu kuma muka fadi a shekarar 2011 to a 2015 ba za mu sake zaben PDP ba,” inji Julius.
Abubakar Sambo, na daga cikin wadanda lamarin ya shafa ya ce abin bakin ciki ne a ce suna ’ya’yan PDP cikakku, kuma suka shiga bala’i saboda zaben Jonathan da PDP, ya sa wasu batagari suka kone musu gidaje aka kashe musu ’yan uwa amma har yanzu an kasa biyansu hakkokinsu.