Zaben kananan hukumomi: ’Yan sanda za su bindige barayin akwatun zabe a Kano
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta sha alwashin bindige duk mutumin da ta kama ya saci akwatin zabe a lokacin zaben kananan hukumomin jihar da za a gudanar a mako mai zuwa. Kwamishinan ’yan sandan Jihar Adenerele Tasheed Shinaba ya bayyana haka a shekaranjiya Laraba lokacin da yake ganawa da wakilan jam’iyyun siyasa game da […]

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta sha alwashin bindige duk mutumin da ta kama ya saci akwatin zabe a lokacin zaben kananan hukumomin jihar da za a gudanar a mako mai zuwa. Kwamishinan ’yan sandan Jihar Adenerele Tasheed Shinaba ya bayyana haka a shekaranjiya Laraba lokacin da yake ganawa da wakilan jam’iyyun siyasa game da matakan tsaro da rundunarsu ke shirin dauka a lokacin zaben kananan hukumomin da za a yi a ranar 17 ga wannan wata.
Kwamishinan ya ce rundunarsa za ta yi duk wani abu da ya kamata wajen tabbatar da cewa an gudanar da zabe na gaskiya. “Ba zan yarda da duk wata harka ta magudi ba, domin an gaya min cewa mutanen Kano ba sa wasa da harkar zabe, don haka za mu yi maganin duk masu shirya magudin zabe. Zan bayar da umarni a harbe duk wanda aka kama da satar akwatin zabe,” inji Kwamishinanan.
Ya yi kira ga ’yan siyasa su ja kunnen magoya bayansu game da irin shirin da rundunar ke yi da kuma matakan da take shirin dauka a lokacin zaben. “A duk duniya dimokuradiyya na
nufin samar da ci gaba, ba wai ta haifar da rigingimu ba. Don haka dole ne a yi komai bisa tsari. Zaben da zai zo, zabe ne mai muhimmmanci da zai nuna matsayin jihar. Mun yi alkawari za mu ba kowa damarsa ta yadda zai yi siyasarsa ba tare da an danne masa hakki ba. Ba zan taba amincewa da siyasar fadace-fadace ba. An kawo ni jihar nan ne don na yi aiki, zan yi kuma kokari wajen yin aikina daidai. Babban abin da za a iya yi min shi ne a zuga a yi min canjin
wurin aiki, to bari na gaya muku cewa ban roki kowa a kan a kawo ni Kano ba,”inji shi.
A jawabansu daban-daban, wakilan Jam’iyyar APC da PDP sun yaba wa kokarin Kwamishinan ’Yan sandan game da matsayin da ya dauka na yin aiki ba tare da goyon bayan wani bangare ba. Haka kuma sun yi alkawarin jan hankalin magoya bayansu kafin ranar zaben.