Zaben Kano: APC tana gaban NNPP da kuri’a 1113

Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta Kasa (INEC) reshen Jihar Kano ta fara tattara tare da sanar da sakamakon zaben gwamna na aka kada a jihar a jiya Asabar. Kafin Hukumar ta tafi hutu ta sanar da sakamakon kananan hukumomi 19. Aminiya ta rawaito cewa Jamiyyar NNPP ta sami nasarar lashe kuriun kananan hukumomi 10 […]

Zaben Kano: APC tana gaban NNPP da kuri’a 1113

Nasiru Yusuf Gawuna

Hukumar Zabe Mai zaman kanta ta Kasa (INEC) reshen Jihar Kano ta fara tattara tare da sanar da sakamakon zaben gwamna na aka kada a jihar a jiya Asabar.
Kafin Hukumar ta tafi hutu ta sanar da sakamakon kananan hukumomi 19.
Aminiya ta rawaito cewa Jamiyyar NNPP ta sami nasarar lashe kuriun kananan hukumomi 10 da suka hada da Karamar Hukumar Rano da Rogo da Wudil da Karaye da Minjibir da Albasu da Gabasawa da Ajingi da Kibiya da Gezawa da Tudunwada.
Haka kuma Jamiyyar APC ta sami nasarar lashe kuriun kananan hukumomin Makoda da Kunci da Tsanyawa da Shanono da Bagwai da Kabo da Warawa da Dambatta.
A gaba dayan sakamakon da aka fadi Jamiyyar APC tana da kuriu 328,040 yayin da Jamiyyar NNPP ta sami kuriu 326,927. Hakan ya sa aka sami tazarar kuriu 1113 tsakanin jamiyyun biyu da ke hamayya da juna a jihar.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu