Zaben Kano: babu wani dalilin soke zabe – APC
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya ce, babu wani dalilin soke zaben jihar da ake gudanarwa a jihar. Shugaban APC ya mayarwa jam’iyyar adawa ta PDP martani, yayin da suka bukaci a soke zaben Gwamnan jihar da ake yi yau. Alhaji Abdullahi, ya watsi da zargin da jam’iyyar PDP ke yi […]
Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya ce, babu wani dalilin soke zaben jihar da ake gudanarwa a jihar.
Shugaban APC ya mayarwa jam’iyyar adawa ta PDP martani, yayin da suka bukaci a soke zaben Gwamnan jihar da ake yi yau.
Alhaji Abdullahi, ya watsi da zargin da jam’iyyar PDP ke yi akan tura `yan daba rumfunan zabe. Ya kuma ce babu wani dalilin soke zaben jihar ganin yadda zabukan ke gudana a jihar.