Zaben Kano: NNPP ta bukaci hukumar shari’a ta binciki kotun daukaka kara

Jam’iyyar NNPP ta bukaci Hukumar Ayyukan Shari’a ta binciki tufka da warwarar da ke cikin hukuncin Kotun Daukaka Kara kan shari’ar zaben Gwamnan Kano

Zaben Kano: NNPP ta bukaci hukumar shari’a ta binciki kotun daukaka kara

Jam’iyyar NNPP ta bukaci Hukumar Shari’a ta binciki tufka da warwara da ta dabaibaye hukuncin Kotun Daukaka Kara kan shari’ar zaben Gwamnan Jihar Kano.

Wani jigo a NNPP, Kwamred Olufemi Ajadi, ya  yi kiran ne bayan kundin hukuncin da kotun ta fitar ya tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf, sabanin hukuncin da kotun ta karanta a zamanta na ranar Juma’a.

Ajadi ya ce binciken ya zama dole ganin yadda kundin hukuncin ke tabbatar da nasarar Gwamna Abba, duk kuwa da cewa a hukuncin da ta karanta da farko ya nuna ta kwace kujerarsa, ta damka wa Nasiru Yusuf Gawuna na Jam’iyyar APC.

Ajadi ya ce akwai bukatar Hukuamr NJC ta yi bincike ta kuma sanar da hakikanin gaskiya, ba a bar jama’a a cikin duhu ba.

“An jefa Kano cikin zaman dar-dar, domin a hukuncin da aka karanta a zauren kotu APC ce ta yi nasara, amma kundin bayanin hukuncin da ta fitar na nuni da cewa Gwamnan Abba Yusuf ne ya yi nasara a karar da ya daukaka. Shin wanne ne gaskiya kuma abin dogaro?

“Al’ummar Najeriya sun yanke kauna daga bangaren shari’a amma duk da haka NNPP ba ta sare ba. Don haka ina kira ga NJC ta bincika ta fito da gaskiya,” in ji.

Ya kuma yi kira ga jama’ar Jihar Kano da su kwantar da hankalinsu su guji tayar da tarzoma.

“NJC da Kotun Koli su sani cewa hankalin duniya ya koma kansu, kuma ina da kwarin gwiwa cewa ba za su ba da kunya ba. NNPP Kanawa suka zaba, kuma babu abin da zai sauya zabin nasu.”

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta