Zaben Kogi: An gano ma’aikatan zabe 30 da suka bace

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta ce, an gano ma’aikatan Hukumar 30 da aka sanar da bacewar su, a wasu rumfunan zabe na zaben Gwamnan jihar Kogi da aka yi jiya Asabar. Rotimi Lawrence Oyekanmi, Sakataren watsa labarai na Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu. Rotimi Lawrence, ya ce a yanzu ma’aikatan suna […]

Zaben Kogi: An gano ma’aikatan zabe 30 da suka bace

Tambarin Hukumar Zabe ta Kasa INEC

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta ce, an gano ma’aikatan Hukumar 30 da aka sanar da bacewar su, a wasu rumfunan zabe na zaben Gwamnan jihar Kogi da aka yi jiya Asabar.

Rotimi Lawrence Oyekanmi, Sakataren watsa labarai na Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu.

Rotimi Lawrence, ya ce a yanzu ma’aikatan suna cikin koshin lafiya ba tare da wani rauni ba, kuma sun isa gidajensu.