Zaben Kogi: APC ta tsayar da Gwamna Bello da wasu ‘yan takara 8
Kwamitin tsare-tsare na jamiyyar APC ya tsayar da Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello da wasu mutum takwas domin fafatawa a zaben fitar da gwani na neman takarar Gwamnan jihar, wanda zai gudana a gobe Alhamis. Sakataren tsare-tsare na Jamiyyar, Malam Lanre Issa-Onilu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a yau. Ya […]
Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello
Kwamitin tsare-tsare na jamiyyar APC ya tsayar da Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello da wasu mutum takwas domin fafatawa a zaben fitar da gwani na neman takarar Gwamnan jihar, wanda zai gudana a gobe Alhamis.
Sakataren tsare-tsare na Jamiyyar, Malam Lanre Issa-Onilu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar a yau. Ya ce mutanen da Jamiyyar ta tsayar sun hada da Gwmana maici na yanzu Yahaya Bello, Hadiza Iyoma Ibrahim, Yahaya Odidi Audu, Sani Lulu Abdullahi da Injiniya Danlami Umar Muhammed. Sauran sune Injiniya Abubakar Bashir, Yakubu Muhammed, Hassan Abdullahi da kuma Miss Ekele Aishat Blessing.
Issa-Onilu, ya ce an tantace ’yan takarar ne bisa duba cancantar su da kwamitin tantancewar ya yi, tare da la’akari da kundin tsarin jam’iyya da kuma dokokin zabe.
Sanarwar ta kara da cewa, akwai mutane bakwai da basu cika ka’idojin tsayawa takarar ba, a don haka kwamitin ya sallame su.
Za a dai a gudanar da babban zaben jihar ta Kogi a ranar 16 ga watan Nuwamba na shekarar da muke ciki, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana.