Zaben Nijar ya gudana cikin lumana a Legas
A karshen makon jiya ne aka gudanar da zabe a kasar Nijar, a inda aka ba ’yan kasar mazauna kasashen waje damar kada kuri’arsu a kasashen da suke gudanar da harkokinsu. Jihar Legas na daya daga cikin jihohin da aka gudanar da zaben, inda aka gudanar da shi a unguwannin Alaba da Gatankowa da Mile […]
A karshen makon jiya ne aka gudanar da zabe a kasar Nijar, a inda aka ba ’yan kasar mazauna kasashen waje damar kada kuri’arsu a kasashen da suke gudanar da harkokinsu. Jihar Legas na daya daga cikin jihohin da aka gudanar da zaben, inda aka gudanar da shi a unguwannin Alaba da Gatankowa da Mile 12 da Koloruwa.
Shugaban Jam’iyar Adawa ta Moden Lumana, Alhaji Bashiru Nuhu, ya shaida wa Aminiya cewa zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali a Jihar Legas duk da kokarin abokan hamayya na kawo cikas.
“Jakadan kasarmu a Najeriya ya so ya kawo tasku a zaben Legas domin ganin sun sami nasara a Najeriya. Ka san duk jam’iyyar da ta yi nasara a Legas ita ce za ta lashe zaben a Najeriya, don haka a ranar Asabar sai Jakadan ya kira mu, ya ce a wuri guda ne za a yi zaben maimakon wurare hudun da aka yi rijistar. Sai muka ce masa in wuri guda ne za a yi, ai za a uzura wa jama’a. Sai ya ce lallai a wuri guda ne za a yi. Hakan ne ya sanya muka yi ta sanar da jama’armu, ganin kwana daya ne kacal ya rage mana daga ranar zaben. Sai muka je gidan radiyo muka yi ta sanar da jama’armu. Da safiyar Lahadi ranar zabe, muka dauki motoci, muka kwaso jama’armu, muka kawo su Alaba, a inda nan ne Jakadan ya ce za a yi zaben. Dab da a fara zaben ne kuma sai ya zo ya ce mana ai kowa a inda ya yi rijistar zai yi zabe. Mu kuma ganin mun kwaso mutanenmu bisa umarnin da ya bayar da fari sai muka nuna tirjiyarmu bisa la’akari da yanayi na cunkoson Legas, domin ta yaya mun kwaso su za mu kuma maida su?” Inji shugaban.
Ya ci gaba da cewa: “Da farko mun nuna tirjiyarmu sai muka gano ashe makarkashiya ce ake neman a kulla mana, a hana mu yin zaben; don an san mu ne da rinjaye. Sai muka yi hanzari muka maida kowa mazabarsa ya kada kuri’arsa kuma cikin ikon Allah muka yi nasara a Legas da kuri’u 851, su kuma jam’iyar tarayya suna da kuri’u 290. Duk da cewa sun fi mu kuri’u a Kano da Fatakwal da Binin, nasarar da muka yi a kansu a Legas sai ta danne duk na wadancan jihohi; ya zamo jam’iyyar Lumana ce ta yi nasara a Najeriya. Mun gode Allah yadda zaben ya gudana lafiya, mun kuma gode wa Gwamnatin Najeriya da irin matakan tsaro da suka ba mu a lokacin wannan zabe.” Inji Bashiru.
Duk kokarin da wakilin Aminiya ya yi domin jin ta bakin shuwagabannin jam’iya mai mulki ta Tarayya abin ya ci tura. Sai dai wakilin ya samu ganawa da wani dan jam’iyyar wanda yake sana’arsa a garin Abekuta, wanda ya yi tattaki ya je Legas ya kada kuri’arsa mai suna Malam Shu’aibu Jikan Godi. Ya shaida wa Aminiya cewa suna fatan nasara, kana suna sa ran Shugaba Muhammadu Yusufu ya lashe zaben, domin ya samu damar karasa kyawawan ayyukan da ya dauko.