Zaben Nijar: ’Yan adawa suna son zama ’yan tawaye

’Yan adawan Jamhuriyar Nijar sun yi barazanar cewa daga ranar 1 ga watan Afrilu “sai dai a kafa gwamnatin riko a kasar” domin su a wajensu daga ranar wa’adin mulkin Shugaba Mahamadou Issoufou ya kare saboda haka ba zai ci gaba da sabon wa’adin mulkin ba.Sun bayyana hakan ne saboda rashin amincewa da sakamakon zaben […]

Zaben Nijar: ’Yan adawa suna son zama ’yan tawaye
Zaben Nijar: ’Yan adawa suna son zama ’yan tawaye

’Yan adawan Jamhuriyar Nijar sun yi barazanar cewa daga ranar 1 ga watan Afrilu “sai dai a kafa gwamnatin riko a kasar” domin su a wajensu daga ranar wa’adin mulkin Shugaba Mahamadou Issoufou ya kare saboda haka ba zai ci gaba da sabon wa’adin mulkin ba.
Sun bayyana hakan ne saboda rashin amincewa da sakamakon zaben da aka yi a kasr. A ranar Lahadin makon jiya ne aka gudanar da zaben Shugaban kasa zagaye na biyu a Jamhuriyar Nijar.
Bayan kammala wancan zaben zagayen farko sai jam’iyyun adawa suka yanke hukuncin mara wa Hama Amadou baya a karkashin gamayyar sauran jam’iyyun da suka sanya wa sunan COPA.
Hakazalika, COPA sun ce ba za su shiga zaben zagaye na biyun ba har sai an saki Hama wanda ke gadon asibiti a kasar Faransa bayan rashin lafiyarsa ya yi tsanani lokacin da yake tsare a gidan yari.
Hukumar Zaben kasar (CENI) wadda Bube Ibrahim ke jagoranta ta sanar da sakamakon zaben a yammacin Talatar da ta gabata, inda ta ce Shugaba Issoufou shi ne wanda ya lashe zaben da kashi fiye da 92 cikin 100, yayin da abokin takararsa ya samu 17 da wani abu cikin 100 kamar yadda hukumar zaben ta bayyana.
Sai dai ’yan adawa sun ce ba su yarda da wannan sakamako ba, bisa hujjar cewa bayan an tabka magudi, kuma ba a samu kashi 50 cikin 100 na yawan kuri’un da aka jefa ba. Wanda shi ne kaso da doka ta tanada don bayyana dan takara a matsayin wanda ya yi nasara.