Zaben Nijar zai iya kai wa zagaye na biyu
Zuwa yanzu da aka bayyana kashi 70 cikin 100 na sakamakon zaben Jamhuriyar Nijar, babu dan takara guda cikin manyan ‘yan takarar biyu (wato Shugaban Kasa Mahamadou Issoufou da kuma Hama Amadou) da ya samu kashi 52 cikin 100 da ake bukata, gabanin Hukumar Zaben Kasar CENI ta bayyana dan takarar da ya yi nasara. […]

Zuwa yanzu da aka bayyana kashi 70 cikin 100 na sakamakon zaben Jamhuriyar Nijar, babu dan takara guda cikin manyan ‘yan takarar biyu (wato Shugaban Kasa Mahamadou Issoufou da kuma Hama Amadou) da ya samu kashi 52 cikin 100 da ake bukata, gabanin Hukumar Zaben Kasar CENI ta bayyana dan takarar da ya yi nasara.
Idan hakan bai samu ba to dan takarar da yafi samun kuri’u da wanda ke biye masa za su je zagaye na biyu a ranar 20 ga watan gobe.