Zaben sabon sakataren kwamitin amintattu na PDP ya gamu da cikas

Karancin ’yan kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ya kawo cikas ga zaben sabon sakataren kwamitin a jiya. Ofishin sakataren kwamitin amintattun ya zama ba a maye gurbinsa ba tun lokacin da tsohon ministan harkokin kasashen wajen, Cif Ojo Madueke ya mutu a shekarar da ta gabata. Wadansu daga cikin membobin kwamitin sun je ofishin jam’iyyar […]

Zaben sabon sakataren kwamitin amintattu na PDP ya gamu da cikas

Karancin ’yan kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ya kawo cikas ga zaben sabon sakataren kwamitin a jiya.
Ofishin sakataren kwamitin amintattun ya zama ba a maye gurbinsa ba tun lokacin da tsohon ministan harkokin kasashen wajen, Cif Ojo Madueke ya mutu a shekarar da ta gabata.
Wadansu daga cikin membobin kwamitin sun je ofishin jam’iyyar da ke Abuja don su zabi sabon sakataren tare da tattauna wadansu batutuwa amma sai suka tarar da wurin taron babu kowa.
Daya daga cikin ’yan kwamitin daga yankin Kudu-maso-Gabas ya fada wa Aminiya cewa taron ba zai cimma barinsa ba saboda rashin halartar sauran membobin kwamitin.