Zaben Shugaban Kasa: Atiku ka bi shawarar da aka ba ka
Zan so a ba ni dama domin in yi kira da kuma tsokaci ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar Shugaban Kasa a zaben bana a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar. Atiku Abubakar dai sananne ne a fagen siyasar Najeriya da aka dade ana damawa da shi a fagen siyasar kasar nan. Bayan […]
Zan so a ba ni dama domin in yi kira da kuma tsokaci ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma dan takarar Shugaban Kasa a zaben bana a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
Atiku Abubakar dai sananne ne a fagen siyasar Najeriya da aka dade ana damawa da shi a fagen siyasar kasar nan.
Bayan ya rike mukamin Mataimakin Shugaban Kasa na tsawon shekara takwas, ya shiga jam’iyyu da dama da zimmar ganin ya mulki kasar nan amma bai samu nasarar yin haka ba.
A bana ne ya samu damar tsayawa takara a babbar jam’iyyar adawa ta PDP inda ya samu lashe jihohi 17 ya sha kaye a hannun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu jihohi 19.
A zaben da mafi yawa daga cikin al’umma da na kasashen waje suke ganin an yi shi cikin adalci da kwanciyar hankali, sai aka wayi gari Alhaji Atiku Abubakar ya yi fatali da sakamakon zaben. Hasali ma ya nuna zai kai kara gaban kotun sauraron kararrakin zabe don a bi masa kadi.
A zargin da Atiku ya yi, ya nuna Jam’iyyar APC ta yi aringizon kuri’u amma bai ce Jam’iyyar PDP ba ta yi magudi a dukkan jihohin da ya samu nasara a zabe ba.
Ina so in janyo hankalin Atiku Abubakar cewa, da Jam’iyyar APC ta yi magudi, ba na tsammanin zai iya samun yawan kuri’un da ya samu a wannan zabe. Sannan ba na jin jihohin Kano da Katsina da Kaduna da sauransu za su kawo yawan kuri’un da ba su kai na zaben shekarar 2015 ba.
Ko ma dai mene ne ya kamata Atiku Abubakar ya dauki dangana. Ya tuna Allah ne ke ba da mulki ga duk wanda Ya so, a kuma lokacin da Ya so.
Idan ya nuna dattaku, kuma ya rungumi kaddara, Allah ne kadai Ya san irin sakayyar da zai yi masa nan gaba.
Kodayake ba laifi ba ne ya tafi kotu don a bi masa kadi, amma ganin yadda manyan kasa irin su Janar Ibrahim Badamasi Babangida da sauransu suka ba shi shawarar kada ya kai kara amma ya yi kunnen uwar shegu ya sa nake ba shi shawarar ya yi karatun ta-natsu don kada ya kawo wa kasar nan koma-baya.
Ya tuna shi da Muhammadu Buhari duk yanki guda suka fito, wato Arewa, don haka kada ya yi wani abu da zai kawo koma-baya ga kasar nan musamman ga Arewa.
Mai girma Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar ina fata za ka dauki wannan shawara tawa da hakan zai daukaka martabarka da a siyasar kasar nan.
Mohammed Sani Shokin
08165280193