Zaben shugabannin Jam’iyyar APC: Abin da ya sa muka kafa kwamiti– Alhassan Jabiru
A kwanakin baya ne Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa ta gudanar da wani taron sirri a gidan gwamnati da ke Lafiya inda shugabanninta suka hallara ciki har da Gwamna Umaru Tanko Al-Makura. Wakilinmu ya gana da tsohon Shugaban Jam’iyyar ACN kuma jigon jam’iyyar Alhaji Suleiman Alhassan Jabiru game da taron da sauran batuttuwa? A kwanaki […]
A kwanakin baya ne Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa ta gudanar da wani taron sirri a gidan gwamnati da ke Lafiya inda shugabanninta suka hallara ciki har da Gwamna Umaru Tanko Al-Makura. Wakilinmu ya gana da tsohon Shugaban Jam’iyyar ACN kuma jigon jam’iyyar Alhaji Suleiman Alhassan Jabiru game da taron da sauran batuttuwa?
A kwanaki kun gudanar da taron shugabannin jam’iyyarku ta APC, Mene ne makasudin taron?
Makasudin taron shi ne Mai girma Gwamnan Jiha Umaru Tanko Al-Makura ne ya kira masu ruwa da tsaki na jam’iyyarmu domin a tattauna. Kamar yadda aka sani masu rikon kwarya na jam’iyyar lokacinsu ya kare, kuma ga lokacin zaben shugabannin jam’iyyar ya kusato. Mun tattauna game da inda ya dace shugaban jam’iyyar ya fito wato daga mazabar Sanata ta Arewa ne ko ta Yamma, domin a Kudu suna da Gwamna Al-Makura. An tattauna a karshe muka amince a kafa wani kwamiti da zai fito da tsarin yadda za a zabi shugabannin jam’iyyar. Wato shi zai tantance cewa shugaba zai fito daga wuri kaza, sakatare zai fito daga wuri kaza da sauransu don kada a karshe wasu yankuna su ce ba a yi musu adalci ba. Mun tattauna abubuwa da dama amma muhimman abubuwan ke nan na bayyana maka.
Wasu na yada jita-jitar cewa kun tashi taron da rikici, yaya gaskiyar lamarin?
A gaskiya ba gaskiya ba ne, duk wanda ya fadi haka dan adawa ne. Kuma kamar yadda ka sani a irin wannan abu wasu ma da ba a gayyace su ba sukan hallara don su lalata kyakkyawan tsarin da matakin da aka dauka a wurin taron. Kowa ya san Jam’iyyar APC jam’iyya ce mai rikon amana da fahimtar juna. Saboda haka batun cewa ba a fahimci juna a karshen taron ba karya ce, magane ce kawai irin ta ’yan adawa. Wadannan ’yan adawa sun kasa gudanar da irin wannan taron gangami na shugabanninsu a jihar nan kamar yadda muka yi, shi ya sa suke ta yada jita-jitar. Babu shakka an tafka muhawara a wurin taron, kowa ya bayyana ra’ayinsa game da batutuwan da aka ambato, amma a karshe an cimma yarjejeniya da fahimtar juna da suka kai ga kafa kwamitin da zai tantace ya fito da tsarin yadda za a fito da shugabannin jam’iyyar.
Shugaba Goodluck Jonathan zai ziyarci jihar nan kwanan nan don karbar wasu da suka canja sheka daga APC zuwa PDP kamar Sanata Solomon Ewuga da Mataimakin Gwamna da sauransu. Ba ka ganin zuwansa ka iya zame wa jam’iyyarku barazana?
Ai zuwan Shugaban kasa Goodluck Jonathan jihar nan kamar tashin tsunsu ne daga wata bishiya zuwa wata. Bai rage wa wancan bishiyar komai ba, haka bai kara wa wancan bishiyar ta biyu komai ba. Goodluck ai ba a maganarsa, yaya za a ce Shugaban kasa ya zo jihar nan alhali mutane na ci gaba da rasa rayukansu. Kwanan nan wani bam ya sake tashi a Nyanya kusa da na da, mutanen da suka mutu suna da dimbin yawa, amma ana yi mana karyar cewa mutum 71 ne suka rasu a bam din farko da ya tashi a Nyanya. Tsakanina da inda lamarin ya auku kilomita daya ne kawai, na ga abin da ya faru da yawan mutane da suka rasu. Ba don Allah Ya kiyaye ba da ni ma bam din ya rutsa da ni. Duk da haka Shugaban kasa washegarin lamarin ya je yana tika rawa a Kano. Saboda haka zuwansa ba zai rage wa jam’iyyarmu komai ba sai dai ya kara mata farin jini da karbuwa a wurin al’ummar jihar baki daya.
Wane kira kake da shi ga magoya bayan jam’iyyarku da al’ummar jihar nan baki daya?
Kiran da zan yi ga magoya bayan jam’iyyarmu mai farin jini shi ne kada su yarda wasu su zo su yaudare su. Allah Ya ba mu Gwamna Umaru Tanko Al-Makura mai son talakawa mai nuna adalci. Saboda haka abin da ya dace su yi shi ne su fito kwansu da kwarkwata su kada kuri’unsu ga Jam’iyyar APC a jihar nan don ba jam’iyyar damar ci gaba da samar musu da ribar dimokuradiyya.