Zaben shugabannin majalisa zai iya kawo wa gwamantin Buhari matsala – Musallah
Alhaji Sadik Ibrahim Musallah shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APGA ta kasa, a tattaunawar da ya yi da wakilinmu ya ce hanyar da aka bi wajen zaben shugabannin majalisun tarayya da aka gudanar a makon jiya za ta iya kawo wa sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari matsala: Aminiya: Me za ka ce kan abin da ya […]
Alhaji Sadik Ibrahim Musallah shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APGA ta kasa, a tattaunawar da ya yi da wakilinmu ya ce hanyar da aka bi wajen zaben shugabannin majalisun tarayya da aka gudanar a makon jiya za ta iya kawo wa sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari matsala:
Aminiya: Me za ka ce kan abin da ya faru a tsakanin Jam’iyyar APC da PDP game da zaben shugabannin majalisun tarayya da aka gudanar a makon jiya?
Sadik Musallahh: To, abin da ya faru a majalisun tarayya kan zaben shugabanninsu musamman Majalisar Dattawa, ya nuna cewa akwai ha’inci ko wata makarkashiya, wadda Akwawun Majalisar Dattawan ya shirya. Domin tunda farko an ce Shugaban kasa, ya nemi ya jinkirta lokacin zaben zuwa karfe 12:00 na ranar da aka gudanar da zaben. Amma ya ki jinkirtawa ya yi amfani da cewa idan aka samu kashi daya bisa uku na yawan ’yan majalisar, za a iya gudanar da zaben.
Haka aka yi aka gudanar da wannan zabe, wanda kusan za mu iya cewa Akawun Majalisar ya ci mutuncin Shugaban kasa. Domin ya nemi a dage saboda ya iso kasar nan ne cikin dare daga tafiya ya kamata a ba shi uzuri, ya tattauna da mutanensa kafin a zo a gudanar da wannan zabe.
Aminiya: Ganin yadda zaben shugabannin majalisar ya kasance yaya kake ganin tafiyar za ta kasance?
Sadik Musallahh: To idan an yi wannan zabe ne bisa kyakyawar niyya za mu iya cewa abin zai yi kyau. Amma idan an yi shi ne bisa wata mummunar manufa abin ba zai yi kyau ba.
Aminiya: Wasu suna cewa kamar Jam’iyyar APC ce ta yi sakaci kan wannan lamari, wato suna cewa ba su dauki darasi kan abin da ya faru ga PDP a zaben shugabannin Majalisar Tarayya na shekara ta 2011 ba?
Sadik Musallahh: Idan aka dubi abin da ya faru kan wannan lamari babu shakka akwai sakacin Jam’iyyar APC a lamarin. Domin ya kamata kafin mako biyu da zuwa ranar da za a gudanar da zaben, a ce ta kintsa gidanta ta shirya domin fuskantar zaben, amma ba ta yi haka ba. Don haka dole ne su samu wannan matsala.
Aminiya: Kana ganin wannan zabe zai iya kawo wa wannan sabuwar gwamnati matsala?
Sadik Musallahh: Babu shakka zaben shugabannin majalisa zai iya kawo wa sabuwar gwamnatin matsala. Domin za a iya amfani da wadannan shugabanni a dakile kokarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Domin abubuwan da ake so su wuce a majalisa, saboda PDP tana adawa za ta iya amfani da ’yan majalisarta a dakile kokarinsa. Kamar abin da yake faruwa a Amurka ne, kan wani kuduri na doka da Shugaba Obama ya kai wa majalisar don saukaka wa al’ummar kasar game da kula da lafiyarsu a asibitocin kasar.
Sai ’yan majalisar da suke adawa da shi, suka dakile wannan kuduri, saboda haka irin wannan za ta iya faruwa a Najeriya. Duk wani kuduri da APC za ta gabatar a majalisa za a iya dakile shi.
Aminiya: To me kake ganin ya kamata Jam’iyyar APC ta yi a kan wannan lamari?
Sadik Musallahh: Abin da ya kamata Jam’iyyar APC ta yi, shi ne ta koma ta kimtsa gidanta, ta dubi ina aka dosa. Bai kamata ta tsaya tana bata lokacin kan muhimman abubuwan da ke gabanta ba.
Ya kamata ta tashi ta taimaka wa Shugaban kasa don tunkarar matsalolin da suke damun kasar nan. Musamman ganin irin yadda al’ummar kasar nan suka fito suka zabi wannan gwamnati da kuma irin adawar da wasu suke nuna wa jam’iyyar.
Aminiya: Wane sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar Najeriya?
Sadik Musallahh: Al’ummar Najeriya su yi hakuri da wannan gwamnati mu ba ta watanni kamar 18 kafin ta fahimci ina aka dosa. Yanzu da farko daga hawan sabuwar gwamnatin nan ta fuskanci yaki da ’yan Boko Haram da yaki da masu cin amanar kasa.
Saboda haka muna fatar ’yan Najeriya za su yi hakuri da wannan gwamnati a raka ta da addu’a kuma kowa ya canja halayensa, idan aka yi haka za a samu nasara.