‘Zaben shugabannin Majalisar Dattawa ya nuna ba a samu canji ba’

Wani jigo a Jam’iyyar APC reshen Jihar Kogi Mista Ben Adaji ya nuna bacin rai kan yadda aka gudanar da zaben shugabanin Majalisar Dattawa, inda ya ce yadda aka gudanar da zaben bai nuna cewa akwai canji a majalisar ba, ta yadda za a samu daidaitawar al’ammuran da ke ci wa jama’a tuwo a kwarya […]

‘Zaben shugabannin Majalisar Dattawa ya nuna ba a samu canji ba’
‘Zaben shugabannin Majalisar Dattawa ya nuna ba a samu canji ba’

Wani jigo a Jam’iyyar APC reshen Jihar Kogi Mista Ben Adaji ya nuna bacin rai kan yadda aka gudanar da zaben shugabanin Majalisar Dattawa, inda ya ce yadda aka gudanar da zaben bai nuna cewa akwai canji a majalisar ba, ta yadda za a samu daidaitawar al’ammuran da ke ci wa jama’a tuwo a kwarya ba.

Ya ce yadda aka gudanar da zabe a majalisar dokoki ta kasa, lallai akwai alamun cewa har zanzu PDP tana nan daram kuma za ta ci gaba da yi wa Jam’iyyar APC zagon kasa. “Jam’iyyar PDP za ta ci gaba da yi wa Jam’iyyar APC bi-ta-da-kulli don kawo cikas ga al’amura a cikin kasa,” inji Adaji.
Mista Ben Adaji ya nuna takaici kan yadda jam’iyya mai mulki wato APC ta bari aka yi mata sakiyar da ba ruwa, ya ce idan jam’iyya mai mulki ba ta yi hattara ba, kila za ta fuskanci barazanar da za ta kawo mata cikas ga shugabancin kasar nan.
Mista Adaji ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu, inda ya ce Jam’iyyar APC ta yi sakaci kwarai da ta bari aka zabi mutanen da suka yi sanadiyyar faduwar tsohon Shugaban kasa a zabe saboda son kansu da rashin shugabanci mai kyau.
Ya ce, maganar yaki da rashawa da cin hanci da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauri niyyar yi yaya zai gudana a yanzu da aka zabi mutanen da ake tuhuma da almundahana.
Adaji ya ce dole ne jam’iyyar ta farka daga barci ta fahimci cewa tana bukatar mutane masu gaskiya ta kowane bangare a cikin wannan gwamnanti don samar da shugabanci nagari.
Mista Adaji ya ce kada Jam’iyyar APC ta ba al’ummar kasar nan kunya ta barin mutanen da ba su da gaskiya su wuce gaba wajen jagorancin muhimman bangarorin gwamnati.
dan siyasar ya ce yaki da rashawa batu ne mai muhimmanci da ba wai jama’ar Najeriya kadai ke son sabuwar gwamnati ta aiwatar ba har ma da sauran kasashen duniya da ke yi wa kasanr nan fatan alheri.