Zaben Taraba: Darius ya dara
Kotun koli ta tabbatar da hukuncin Kotun daukaka kara wadda ta tabbatar da zaben Mista Darius Ishaku a matsayin Gwamnan Jihar Taraba.Kotun ta yi watsi da karar da ’yar takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC Hajiya A’isha Jummai Alhassan ta yi, saboda rashin cancantar hakan.A jiya Alhamis ne Kotun kolin ta tabbatar da zaben Gwamna […]

Kotun koli ta tabbatar da hukuncin Kotun daukaka kara wadda ta tabbatar da zaben Mista Darius Ishaku a matsayin Gwamnan Jihar Taraba.
Kotun ta yi watsi da karar da ’yar takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC Hajiya A’isha Jummai Alhassan ta yi, saboda rashin cancantar hakan.
A jiya Alhamis ne Kotun kolin ta tabbatar da zaben Gwamna Darius Ishaku. Kuma za a bayyana dalilin yanke wannan hukunci ne a ranar 22 ga Fabrairu mai zuwa a cewar kotun.
“Ina da yakinin babu hujjar daukaka wannan kara. Don haka na yi watsi da ita,” inji Mai shari’a Bodeh-Rhode bibore, wanda ya karanta babban hukuncin alkalai bakwai suka zauna a kan shari’ar. “An tabbatar da hukuncin Kotun daukaka kara kuma an tabbatar da zaben wanda ake kara na farko a matsayin Gwamnan Jihar Taraba,” inji alkalin.
Hajiya A’isha Alhassan ta tafi Kotun kolin ne dauke da bukatu hudu na kalubalnatra hukuncin Kotun daukaka kara, wadda ta soke nasarar da Kotun Zabe ta Jihar Taraba ta ba ta.
Alkalai biyar da suka yi zama a Kotun daukaka kara da ke Abuja a ranar 31 ga Disamban bara, sun soke hukuncin Kotun Zabe ta Jihar Taraba wadda a ranar 7 ga Nuwamban bara ta bayyana A’isha Alhassan a matsayin wadda ta lashe zaben 11 ga Afrilun bara a jihar.
Kotun Zaben ta yanke hukuncin cewa dan takarar Jam’iyyar PDP, Mista Darius Ishaku ba a zabe shi domin tsayawa takara a Jam’iyyar PDP ba, don haka bai cancanci tsayawa a wancan zabe ba.
Lauyan ‘’yar takarar ta APC, Abiodun Owonikoko ya shaida wa Kotun kolin a jiya Alhamis cewa dalilin hukuncin kotun farkon ya dogara ne kan muhimmin abin da zai ba jam’iyya tsayar da dan takara a wani zabe, a karkashin tsarin mulki wajibi ne ya kasance an gudanar da zaben fidda gwani a karkashin wata jam’iyya kuma a karkashin tsarin mulki hakan yana nufi zaben fidda gwani a jam’iyyar da za a tsaya takara. Ya kawo hujjoji da misalai kan wasu shari’u da suka gabata don tabbatar da da’awarsa.
Sai dai lauyan Gwamna Ishaku, Mista Kanu Agabi, ya ce a hukuncin Kotun daukaka karar ta nuna cewa Jam’iyyar APC ta fadi a sakin layi na uku na bukatarta cewa Mista Ishaku dan Jam’iyyar PDP kuma dan takarar PDP ne a zaben na 11 ga Afrilun bara a jihar. Kuma masu daukaka karar sun sha nanata cewa wanda ake kara na farko dan takarar PDP ne, kuma sun gabatar da shaidu 51 gaban kotun farko wadanda ba a dadale su ba.
Shi ma lauyan Jam’iyyar PDP Mista Solo Ahmed ya ce jam’iyyar ba taba musanta cewa Mista Ishaku dan takararta ne ba. Y ace masu daukaka kara sun ce ba a yi zaben fidda gwani ba, amma suka ci gaba da cewa an gudanar da (zaben fidda-gwanin) ne a Abuja.
Ya ce, hukuncin kotuna da Owonikoko ya gabatar sun nuna cewa batun da ya shafi zaben fidda gwani, lamari ne da ’ya’yan jam’iyyar da hakan ta faru da su za su tuhuma ko kuma Hukumar INEC.
Lauyan Hukumar INEC, Mista Joseph Daudu, ya amince da hujjojin da Lauya Ahmed ya gabatar game da matsayin APC kan batun zaben fidda gwani na PDP.
Ya ce da’awar APC cewa ba a yi zaben fidda gwani ba, ya rushe ta bayyana cewa a Abuja a gudanar da zaben fidda gwani.