Zaben Tunisiya: Marzouki ya ki amincewa da shan kaye

Mutumin da ya zo na biyu a zaben Shugaban kasar Tunisiya wanda aka gudanar ranar Lahadi, Moncef Marzouki, ya ki amincewa da shan kaye bayan an bayyana Mista Beji Caid Essebsi a matsayin zakara a zaben.Mista Marzouki wanda kuma shi ne shugaban gwamnatin rukon kwarya ya ce bayyana Mista Essebsi a matsayin wanda ya yi […]

Zaben Tunisiya: Marzouki ya ki amincewa da shan kaye
Zaben Tunisiya: Marzouki ya ki amincewa da shan kaye

Mutumin da ya zo na biyu a zaben Shugaban kasar Tunisiya wanda aka gudanar ranar Lahadi, Moncef Marzouki, ya ki amincewa da shan kaye bayan an bayyana Mista Beji Caid Essebsi a matsayin zakara a zaben.
Mista Marzouki wanda kuma shi ne shugaban gwamnatin rukon kwarya ya ce bayyana Mista Essebsi a matsayin wanda ya yi nasara ba dimukradiyya ba ne. Masu sukar zababban shugaban suna kafa hujja da cewa ya taba aiki a tsohuwar gwamnatin Shugaba Zine el-Abedine Ben Ali.
An dai habarar da Mista Ben Ali ne a shekarar 2011 bayan wani juyin juya halin da ya kawo karshen mulki shugabannin kasashen Larabawa da dama a yankin.
A wani dan takaitaccen jawabi da ya yiwa magoya bayansa da suka taru a kofar hedkwatar ofishin yakin neman zabensa, Mista Essebsi ya yi kira ga ‘yan kasar da su hada kansu.
Har ila yau, sabon shugaban mai shekara 88, ya taba yin aiki da Shugaban kasar na farko bayan samun ’yancin kai, Habib Bourguiba. Kuma ya samu nasara a zaben ranar Lahadin ne da fiye da kashi 55 cikin dari na kuri’un da aka kada. Wannan ya sa ya zama shugaban kasa na farko da aka zaba a turbar dimokaradiyya a kasar.