Zaben Zimbabwe: Zan kada Mugabe – Tsbangirai

Babban abokin adawar Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe Morgan Tsbangirai ya yi ikirarin samun gagarumar nasara domin kawo karshen shugabancin da ya shafe shekara 33 yana yi.Tsbangirai ya bayyana haka ne lokacin da yake kada kuri’arsa a Harare babban birnin kasar a shekaranjiya Laraba, inda ya ce yana da yakinin yana da goyon bayan da […]

Zaben Zimbabwe: Zan kada Mugabe – Tsbangirai

Zimbabwe’s President Robert Mugabe casts his vote as his wife Grace and daughter Bona (L-R) look on in Highfields outside Harare July 31, 2013. Zimbabweans voted in large numbers on Wednesday in a fiercely contested election pitting veteran President Robert Mugabe against Prime Minister Morgan Tsvangirai, who has vowed to push Africa’s oldest leader into […]

Daga hagu Shugaba Mugabe da babban abokin adawarsa Roman Tsvangirai suna kada kuri’a a shekaranjiya LarabaBabban abokin adawar Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe Morgan Tsbangirai ya yi ikirarin samun gagarumar nasara domin kawo karshen shugabancin da ya shafe shekara 33 yana yi.
Tsbangirai ya bayyana haka ne lokacin da yake kada kuri’arsa a Harare babban birnin kasar a shekaranjiya Laraba, inda ya ce yana da yakinin yana da goyon bayan da zai kada abokin adawarsa.
Mutanen Zimbabwe sun yi jijjifin fita rumfunan zabe domin kada kuri’arsu, a zaben da masu sanya ido na kasashen Afirka suka ce babu wasu manyan matsaloli, duk da zargin magudi da zurmuken kuri’u.
 Shugaba Mugabe ya sha nanata cewa zaben zai gudana bisa gaskiya da adalci. Kuma ya I alkawarin zai ‘mika wuya’ idan sakamakon zaben ya nuna ya sha kasa.
Sai dai mutane da dama ba su amince da wannan matsayi na Shugaba Mugabe ba, inda hatta Tsbangirai ma ya ce yana kallon alkawari na Mugabe a matsayin romon baka ne kawai.
Zargi na baya-bayan nan game da magudin zaben ya fito daga nazarin da wata cibiya mai suna Research and Adbocacy Unit wadda ta ce cikin wadanda aka tsara za su jefa kuri’a har da matattun mutane miliyan daya ko kuma mutane da suka yi kaura daga kasar.
Masu jefa kuri’a sun nuna haba-haba da zaben, inda suka rika dogon jerin gwano yafe da barguna tun kimanin awa hudu kafin a bude rumfunan zabe.
 daruruwan mutane sun yi ta jira domin su jefa kuri’a a cikin tantuna a Mbare, tsohon garin da ke babban birnin kasar Harare.
Waa mai shekara 66 mai suna, Ellen Zhakata, ta ce, “Ina cike da farin cikin jefa kuri’ata. Ina so ne a kawo karshen matsala a kasarmu.”