Zafi ya hallaka mutane 800 a Pakistan
Mutane kimanin dari takwas ne suka hallaka a ‘yan kwanakin nan, sakamakon cucuttukan da ke nasaba da matsanancin zafi a yankin Kudancin Pakistan inda ake zafin da ya kai maki 45 a ma’aunin Celsius, madadin maki 26 a yanayin da yake ba zafi, ba sanyi. Ana fama da wannan yanayi na zafi ne a daidai […]
Mutane kimanin dari takwas ne suka hallaka a ‘yan kwanakin nan, sakamakon cucuttukan da ke nasaba da matsanancin zafi a yankin Kudancin Pakistan inda ake zafin da ya kai maki 45 a ma’aunin Celsius, madadin maki 26 a yanayin da yake ba zafi, ba sanyi.
Ana fama da wannan yanayi na zafi ne a daidai lokacin da al’ummar Musulmi ke azumin watan Ramadan. Kodayake, malaman addinin sun ba da fatawar cewa masu aikin karfi a wannan yanayin za su iya shan azumin, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito.
karin mutanen dai sun mutu ne sakamakon galabaitar da suka yi a asibitocin da ke birnin Karachi, wurin da ya fi kamari. A shekaranjiya Laraba likitocin sun ce sun shiga damuwa kan yadda matsalar ta kara ta’azzarara a rana ta biyar.
Asarar rayukan ta kara tsananta ne saboda tsawon lokacin da aka dauka babu wutar lantarki ga kuma matsanancin karancin ruwan sha. Akasarin wadanda abin ya fi shafa tsofaffin ne daga iyalai marasa galihu.
Mahukuntan lardin Sindh da kuma gwmnatin kasar a Islamabad na zargin junasu kan abkuwar lamarin.
Jama’a da dama na nuna fushinsu a fadin kasar kan abin da suka ce gazawar mahukuntan wajen tashi tsaye su kare rayukan jama’a.
Ko a karshen watan jiya, sai da irin wannnan yanayin zafin ya hallaka mutane fiye da 1,500 a kasar Indiya, wadda take makwabtaka da Pakistan din.