‘Zafin kishi’

Barkanmu da warhaka Manyan gobe. Yaya zafi? Tare da fatan ana yawan shan ruwa kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘zafin kishi’. Labarin ya kunshi yadda yawan kishi ke sanya mutum halaka. A sha karatu lafiya. Aina’u ta kasance mai matukar kaunar mijinta da kuma zafin kishi. Duk da cewa […]

‘Zafin kishi’
‘Zafin kishi’

Barkanmu da warhaka Manyan gobe. Yaya zafi? Tare da fatan ana yawan shan ruwa kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘zafin kishi’. Labarin ya kunshi yadda yawan kishi ke sanya mutum halaka. A sha karatu lafiya.

Aina’u ta kasance mai matukar kaunar mijinta da kuma zafin kishi. Duk da cewa ita ce uwargida, komai maigidan ya kawo sai ya fara ba ta kafin ya kaiwa amaryarsa, amma hakan bai gamsar da ita ba har alkawari ta dauka na cewa wata rana za ta fitar da amaryar daga gidan mijin saboda kishi.
Maigidansu na iya kokarinsa wajen kamanta adalci a tsakanin matansa biyu. Ran nan sai ya samu labarin cewa Aina’u na dauke da juna biyu. Hakan ta sa ya cigaba da ba ta kyakkyawar kulawa kuma har ya fadawa mahaifiyarsa halin da ake ciki na cewa Aina’u ta samu juna biyu.   Saboda murna sai mahaifiyarsa ta ba shi wani zobe ta ce ya kai wa amaryarsa Aina’u amma kada ya ba ta, ya bari sai cikin ya girma.
Da ya iso gida ya baiwa amaryar ta adana masa kuma ya ce mata kada ta bari Aina’u ta sani. Ashe Aina’u na makale a kofa tana jin su. Bayan amarya ta boye zoben, Aina’u ta shiga dakin amarya ta sace zoben. Ta tafi teku har sai da ta kai tsakiyar ruwan sannan ta jefa zoben.
Bayan ’yan watanni, maigida ya ce da amaryarsa ta kawo zobe, sai ta shiga nema ba ta gani ba. Sai ya ce mata ta yi masa girkin miyar kifi zai fita amma ta nemo zoben kafin ya dawo.
A cikin damuwa ta shiga kasuwa ta sayo kifi. Da ta dawo gida yanka kifi sai ga wannan zoben a cikin kifin sai ta boye ta yi shiru.  Da maigida ya ce ta kawo sai ta fitar da zoben, ganin hakan ya sa Aina’u ta yanke jiki ta fadi a sume.  Bayan ta farfado ne sai ta fadi gaskiyar yadda al’amarin ya kasance kuma ta nemi mijin ya yafe mata amma sai ya ki yarda sai da ya sake ta don ya zama darasi a gareta.
Manyan gobe, kun ji illar zafin kishi, inda ya kai Aina’u ya baro.