Zaftarewar ƙasa ta kashe mata masu haƙar zinare a Mali
Ajali ya rutsa da su ne a cikin wani rami mai ruwa da laka, inda zaftarewar ƙasar ta binne su a ciki
Masu haƙar zinare aƙalla mutum 10 sun mutu wasu da dama sun ɓace bayan zaftarewar ƙasa a kansu a wani filin haƙar ma’adinai yankin Koulikokro na ƙasar Mali.
Hukumomin yankin sun bayyana cewa mata ne yawancin masu haƙar zinaren da abin ya rutsa da su mata ne, kuma an kasa ciro gawarwakinau, “saboda tsananin sarƙaƙiyar yanayin.”
Gwamnatin yankin ya bayyana cewa ajali ya rutsa da su ne a ƙauyen Danga, a cikin wani rami mai ruwa da laka, wanda zaftarewar ƙasar ta binne su a ciki a ranar Laraba.
Ta bayyana a shafinta na Facebook cewa “abin takaicin shi ne babu ko mutum ɗaya da ya tsira a cikin su.”
Jami’in kula da haƙar ma’adanai a yankin, Ousmane Diakite, ya bayyana cewa, “akalla mutum 10 ne abin ya yi alajinsu.”
Wani jami’in gwamnati da ya nemi a bole sunansa ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa akwai yiwuwar adadin zai karu, a yayin da hukumomi ake ci gaba aikin ceto.
Magajin wani gari da ke maƙwabtaka da Koulikokro, ya bayyana wa AFP cewa, “babu wanda ya tsira bayan faruwar lamarin.”
Mali na daga cikin ƙasashe mafiya talauci a duniya, duk da cewa tana cikin ƙasashen mafiya arzikin zinare a nahiyar Afirka.
Zaftarewar ƙasa na yawan halaka masu haƙar zinare a ƙasar, a yayin da hukumomi ƙasar ko ƙoƙarin kawo ƙarshen amfani da hanyoyin gargajiya wajen gudanar da harkar.
A watan Janairun 2024 zaftarewar ƙasa ta kashe masu halartar zinare 70 a wurin da na ranar Larabar nan ya faru.