Zaftarewar kasa ta kashe mutum 23 a Kamaru

Daga cikin mutanen da suka rasa rayukan su akwai yaro daya.

Zaftarewar kasa ta kashe mutum 23 a Kamaru

Akalla mutane 23 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa biyo bayan shatata ruwan sama da aka yi a yammacin jiya Lahadi a birnin Yaoundé, babban birnin kasar Kamaru.

Birnin na Yaounde na daga cikin yankunan da ake fuskantar rushewar gidaje jefi-jefi a duk lokacin da aka samu mamakon ruwan sama, ganin yadda birnin yake zagaye da tsaunuka da gangara ba tare da an ayi aiki da tsari gina gidaje yada ta kamata.

Iftil’ain da ya faru a gundumar Mbankolo, da ke wajen Arewa maso Yammacin birnin Yaoundé, kuma ya faru ne sakamakon fashewar wata madatsar ruwa a wani tafki na wucin gadi kamar dai yadda kafafen yada labaren kasar suka ruwaito.

Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Kasar, David Petatoa Poufong ya shaida wa manema labarai a safiyar yau Litinin cewa ma’aikatan hukumar sun samu nasarar zakulo gawarwakin mutane 15 a jiya kuma da safiyar yau Litinin sun gano wasu matatun 8.

Wani jami’in kwana-kwana a wurin da al’amarin ya faru ya bayyana cewa daga cikin mutanen da suka rasa rayukan su akwai yaro daya.

Jami’an tsaro na kokarin nesanta fararen hula daga ainihin wurin da zaizayar kasa ta afku tare da dasa shingen tsaro.

Gani girman wannan barna kasancewa ruwan ya kwashe duk wani abu da ke kan hanyarsa, Daouda Ousmanou, shugaban sashin II na Yaoundé inda Mbankolo yake, ya isar da kira ga jama’a na su yi hattara wajen gina gidaje.

A ranar 27 ga Nuwamba, 2022, akalla mutane 15 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a wani yanki na tudu da ke gundumar Damascus, kudancin Mbankolo.

Kwamishina ya yi murabus bayan sauya masa ma’aikata a Kano

Gobara ta ƙone shaguna 50 a kasuwar kara a Sakkwato

An yi canjaras tsakanin Liverpool da Manchester United

Tinubu zai tafi Ghana rantsar da John Mahama