Zagayen da PDP ke yi rashin girmama wadanda ake kashewa ne – Sanata Musa
Sanata Ibrahim Musa, shi ne Sanata mai wakiltar Neja ta Arewa a Majalisar Dattawa, kuma shi ne, shugaban kwamitin riko na Jam’iyyar APC a Jihar Neja. A hirarsa da Aminya ya soki zagayen da shugabannin Jam’iyyar PDP ke yi na gangamin shiyyoyi da cewa rashin girmama rayukan wadanda ake kashewa a jihohin Borno da Yobe […]
Sanata Ibrahim Musa, shi ne Sanata mai wakiltar Neja ta Arewa a Majalisar Dattawa, kuma shi ne, shugaban kwamitin riko na Jam’iyyar APC a Jihar Neja. A hirarsa da Aminya ya soki zagayen da shugabannin Jam’iyyar PDP ke yi na gangamin shiyyoyi da cewa rashin girmama rayukan wadanda ake kashewa a jihohin Borno da Yobe ne:
Me za ka ce dangane da taron shiyyar Arewa ta Tsakiya da Jam’iyyar PDP ta gudanar a Minna?
Abin da zan ce shi ne, taron ya zama hanya ce ta almubazzzaranci da shirme da rashin sanin ya kamata. Dalili, idan aka dubi halin da shiyyar Arewa maso Gabas ke ciki, amma a ce ana wannan abin Shugaban kasa bai kula ba, sai yawace-yawace a garuruwa yana tara jama’a ana raye-raye.
Ba ka ganin Shugaba Jonathan na da Babban Hafsan Tsaro da Ministan Tsaro da ya ba alhakin shawo kan lamarin?
Idan ka je kasar da shugabansu ya san abin da yake yi, ya kamata a ce yanzu muna cikin halin makoki ne domin rayukan bayin Allah da ba su ji ba, ba su gani da aka kashe su. Wadannan abubuwan da suke yi ba abubuwa ne da dan Adam din da ya san abin da yake yi, zai yi su ba.
Shin Jam’iyyar ba ta da ’yancin gudanar da gangamin ne ganin jam’iyyarku ta APC, ba ta zauna ba?
Sun ce suna da farin jini da jama’a, kuma su ke cin zabe kullum. In haka ne, bai kamata su rika hana idonsu bar ci suna yawace-yawace ba. Ina kara tuna maka abin da ke faruwa a jihohin Adamawa da Borno da Yobe, in a wata kasa ce da shugaban kasa ya san abin da yake yi, sai ya sauka daga mulki saboda ya kasa tabbatar da tsaro.
Me za ka ce game da zargin da PDP ta yi cewa farin jinin APC ya tsaya ne a kafofin watsa labarai shi ya sa a kusan kullum kuke rasa wasu daga cikin jigajiganku?
Wannan maganar banza ce. Da farko sun je Kwara da suka je karya kawai suka yi ta shara wa jama’a. Ita wannan ’yar gidan Saraki mai suna Rukayya Gbemisola ba ta taba yin Jam’iyyar APC ba. Haka kuma da suka je Jihar Imo suka yi ta kame-kamensu a gaban jama’a suka rasa abin da za su gaya musu. Sanata Chris Anyawu ba ta taba yin APC ba, Babban Lauya Mike Ahamba ya dade da barin CPC. Babban abin da ke damunsu shi ne APC. Maganar wadanda suka bar jam’iyyar, kamar tsohon Gwamnan Jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau da takwaransa na Sakkwato Alhaji Attahiru dalhatu Bafarawa, Shekarau mutum ne da ya yi ta zagin PDP a baya. Shi kuma Bafarawa, wa ke maganarsa a siyasar Sakkwato?
Idan nan gaba wadannan mutanen suka nuna sha’awar komawa APC, za ku amshe su?
In ka duba Shekarau ya dade yana yi wa Jam’iyyar ANPP munafunci. Da ma muna da masaniyar cewa ba za a yi tafiya mai nisa da su ba a wannan sabon lalen. Ba muatne ne masu amana ba a harkokinsu.